Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana rasuwar mataimakin sufeto janar na 'yan sanda na ƙasa mai ritaya, DIG Abdulkadir Danwawu Fagge d...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana rasuwar mataimakin sufeto janar na 'yan sanda na ƙasa mai ritaya, DIG Abdulkadir Danwawu Fagge da cewa babban rashi ne ga al'ummar jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara CP. Ibrahim Balarabe Maikaba ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya rasuwar Marigayin a Unguwar Fagge ta Kano.
Ya yi nuni da cewa a matsayin Marigayin na yayan su kuma abokin aikin su, mutum ne na ƙwarai mai gaskiya da haƙuri da taimakon al'umma, domin shi ne ya taimake su da suka shiga aikin dan sanda yana cikin aikin suka zo suka same shi.
CP. Ibrahim Balarabe Maikaba ya ƙara da cewa babban rashi ne ga al'ummar Fagge domin, jihar Kano ma, ta daɗe ba ta sami wanda ya kai matsayin DIG ba, sai a lokacin sa tun bayan Maye Bashir Wali da ya yi DIG, sai kuma yanzu akwai ɗan asalin Garko, Sadik .
Daga ƙarshe Kwamishinan ya yi fata da addu'ar Allah ya raya zuriyar marigayi DIG Abdulkadir Dawawu ya kyautata bayan sa, 'yan uwan sa da mata da su a'lummar Fagge, Allah ya ba su haƙurin juriyar wannan babban rashi.

No comments