Daga Khalid Idris Doya 'Yan fashin daji (Bandits) sun kashe 'yan Sanda biyar a wani musayar wuta da suka yi a ƙauyen Sabon Sara da ...
Daga Khalid Idris Doya
'Yan fashin daji (Bandits) sun kashe 'yan Sanda biyar a wani musayar wuta da suka yi a ƙauyen Sabon Sara da ke cikin ƙaramar hukumar Darazo a jihar Bauchi.
'Yan Sanda da aka kashe sun haɗa da DSP Ahmad Muhammad (SID), ASP Mustapha Muhammad (10 PMF), Insifekta Amarhel Yunusa (10 PMF), Insifekta Idris Ahmed (10 PMF) da kuma Kufural Isah Muazu (AKU).
Yayin da kuma Insifekta Isah Musa (SID) da Insifekta Yusuf Gambo (SID), suka gamu da munanan raunuka sakamakon kwantan ɓauna da aka kai musu a lokacin da suke aikin sintiri.
A wata sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yansandan jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewar a ranar 22 ga watan Nuwamban 2025 ne suka samu rahoton aikace-aikacen wasu da ake zargin Fulani ne masu ɗauke da makamai a yankin.
A cewar Wakil, bayan samun rahoton an haɗa tawagar jami'ai wanda suka ƙunshi sashin kai ɗaukin gaggawa (RRS), jami'an sintiri, Mobile Police 10 PMF, sashin yaƙi da masu garkuwa da mutane (AKU), da kuma sashin binciken manyan laifukan (SID), inda suke kan gudanar da aikin sintiri a sirrince domin daƙile rikicin manoma da makiyaya kwatsam sai aka musu kwantan ɓauna.
A cewarsa an samu musayar wuta sosai a tsakanin 'yan bindigan da 'yansandan inda su ma 'yansandan sun kashe barayin dajin da daman gaske.
Bayan kwantan ɓauna, an tura ƙarin tawaga domin ta dafa wa 'yansandan da aka yi musu kwantan ɓauna inda aka samu nasarar kwaso gawarwakin 'yansandan da wadanda aka jikkata zuwa babban asibitin Darazo.
Wakil a halin yanzu ana ta ƙoƙarin bin sawun ɓata-garin da nufin ganin an kamosu, inda suka bai wa jama'a tabbacin cewa rundunar za ta yi dukkanin mai yiwuwa domin ganin an cafko waɗanda suka kashe 'yansandan.
Kwamishinan 'yansandan jihar Bauchi CP Sani-Omolori Aliyu, ya kai ziyara domin gane wa idonsa abubuwan da suka faru tare da miƙa ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Ya jaddada aniyar rundunar na ci gaba da kare rayuwa da dukiyar al'ummar jihar.

No comments