Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Bauchi Ta Rufe Dukkanin Makarantu Kan Barazanar Tsaro

Daga Khalid Idris Doya  Gwamnatin jihar Bauchi ta bada umarnin a gaggauta rufe dukkanin makarantu kama daga Firamare, sakandare da manyan ma...


Daga Khalid Idris Doya 

Gwamnatin jihar Bauchi ta bada umarnin a gaggauta rufe dukkanin makarantu kama daga Firamare, sakandare da manyan makarantun gaba da sakandare da suke sassan jihar ciki kuwa har da makarantun gwamnati da na masu zaman kansa, ta ce saboda barazanar tsaro. 

Wannan bayanin na ƙunshe ne ta cikin sanarwar manema labarai da jami'in hulɗa da jama'a na ma'aikatar ilimi ta jihar Bauchi Jalaludeen Usman da ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta misalta matakin a matsayin mawuyaci amma ya dama dole ne, ta ce bayan shawarori da aka samu daga masu ruwa da tsaki da nufin kare ɗalibai da malamansu da kuma makarantu baki ɗaya ne ya sa aka cimma matsayar rufe makarantun. 

"Gwamnati tana cike da masaniyar rashin jin daɗi da wannan matakin ka iya haifarwa," sanarwar ta ci gaban da cewa.

"Amma, kare 'ya'yanmu na daga cikin babban nauyin da ke kanmu. Kowani ɗalibi a Bauchi ya cancanci koyon karatu a yanayi mai tsaro, aminci da kwanciyar hankali ba tare da firgici ba," inji sanarwar. 

Don haka ne gwamnatin ta roƙi iyaye, masu kula da yara, masu mallakin Makarantu, da masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankula tare da bai wa gwamanti haɗin kai wajen ganin matakan da jami'an tsaro ke ɗauka na ganin an shawo kan barazanar tsaro sun kai ga nasara. 

"Muna neman jama'a da su bayar da haɗin kai ɗari bisa ɗari. Idan ka ga wani abu ka gaggauta faɗi. Bayar da rahoto a kan lokaci daga wajen jama'a na da gayar alfanu wajen kare al'ummar mu," sanarwar ta ƙara faɗi.

Gwamnatin ta bayar da tabbacin cewa za ta sanar da jama'a halin da ake ciki da kuma lokacin da za a koma harkokin makaranta da zarar komai ya tafi yadda ake so. 

Idan za a tuna dai jihohi da dama sun ɗauki matakin kulle Makarantu sakamakon garkuwa da ake yi da ɗalibai a 'yan baya-bayan nan a wasu jihohin Arewa.
 

No comments