Gwamnatin Jihar Kaduna ta ƙara jaddada ƙudirin ta na jawo masu zubair jari na ƙasa da ƙasa zuwa jihar, Wanda hakan zai ƙara bunƙasa tattalin...
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ƙara jaddada ƙudirin ta na jawo masu zubair jari na ƙasa da ƙasa zuwa jihar, Wanda hakan zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin Ta.
Yayin da ya ke gabatar da Jawabi a taron ƙoli na manyan ‘Yan Kasuwa na Daniya, Wanda ya gudana a ƙasar Afrika ta Kudu, Gwamna Uba Sani ya gabatar da jihar Kaduna a matsayin jihar da ta fi dacewa wajen zuba jari a Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki ya fitar, ya ce taron wanda Hukumar Kula da Zuba Jari ta Nijeriya (NIPC) da Ofishin Jakadancin Nijeriya, tare da haɗin gwiwar MTN suka shirya ya samu halartar manyan masu zuba jari na duniya, da jami’an gwamnati na matakai daban-daban.
A cewar sanarwar, Gwamna Uba Sani ya gabatar da Jihar Kaduna a matsayin jihar da ta fi dacewa da zuba jari a Nijeriya, wadda aka gina bisa sauye-sauyen manufofi, kwanciyar hankalin, dokoki da yanayin kasuwanci mai sauƙi. Ya bayyana muhimman fannonin zuba jari guda huɗu kamar Noma, Sufuri, Ma’adinai da Makamashin Sabuntawa samar ginshiƙan dabarun ci gaban jihar.
“Mu’amalar Gwamna Uba Sani a Taron G-20 ta ƙara tabbatar da matsayin Kaduna a matsayin cibiyar zuba jari mai inganci. Yawancin manyan masu zuba jari na duniya sun nuna sha’awar shiga harkoki a fannonin da muka fifita,” in ji sanarwar.
Gwamnan ya kuma gana da shugabannin , wata masana’antar tace ƙarafa masu daraja da ke Afirka ta Kudu. PMT Inda ta gabatar da tayin haɗin gwiwa ta hannun Kamfanin Samar da Ma’adinai na Kaduna (KMDC) domin tallafawa ma’adinan gargajiya da fasaha, gina ƙwarewa, da aiwatar da shirin kafa cibiyar tarawa da sarrafa ma’adinai a Kaduna.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan ya tabbatar da cewa ƙofar Kaduna a bude take ga masu zuba jari na gari, waɗanda ke bin ka’idoji masu dorewa tare da mayar da hankali kan samar da darajar dogon lokaci.
“Jihar Kaduna za ta ci gaba da zurfafa sauye-sauyen da ke sauƙaƙa kasuwanci da jawo masu zuba jari masu ƙima waɗanda za su samar da ayyukan yi da dama ga mutanenmu,” in ji shi.
Hakazalika, sanarwar ta kuma ruwaito Gwamna Uba Sani yana yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa sauye-sauyen da suka inganta yanayin zuba jari a Nijeriya tare da ƙarfafa jihohi wajen neman haɗin gwiwar ƙasashen duniya.

No comments