Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojoji Sun Karɓi Mulki A Guinea-Bissau

Sojoji a ƙasar Guinea‑Bissau sun bayyana cewa sun karɓi cikakken iko da mulkin ƙasar, tare da dakatar da dukkanin harkokin zaɓe da kuma rufe...



Sojoji a ƙasar Guinea‑Bissau sun bayyana cewa sun karɓi cikakken iko da mulkin ƙasar, tare da dakatar da dukkanin harkokin zaɓe da kuma rufe iyakokin shiga da fita. Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan gudanar da zaɓukan ’yan majalisa da na shugaban ƙasa a ƙasar.

Tun da sanyin safiyar Laraba, an ji karar harbe-harben bindiga a kusa da fadar shugaban ƙasa da ke Bissau, babban birnin ƙasar, inda aka hangi wasu sojoji sanye da kayan aiki suna karɓe babbar hanyar da ke kaiwa fadar.

Jaridar labarai ta duniya AFP ta ruwaito cewa sojojin sun karanta wata sanarwa a helkwatar rundunar sojin ƙasar da ke Bissau, inda suka tabbatar da cewa sun karɓi “cikakken iko” da dukkanin harkokin mulki.

A cikin sanarwar, sojojin sun ce an dakatar da tsarin zaɓe gaba ɗaya, kana an ɗauki matakin kulle iyakokin ƙasar domin tabbatar da tsaro. Sai dai ba su bayyana ko wane dalili ne ya sa suka dauki wannan mataki ba, haka kuma ba su ambaci makomar shugabannin gwamnatin da aka zaba ko ake shirin zaba ba.

Guinea-Bissau na ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka ta Yamma da ke yawan fuskantar juyin mulki da rikice-rikicen siyasa tun bayan samun ’yancin kai, lamarin da ya daɗe yana raunana tattalin arzikinta da tsarin dimokuraɗiyya.

Har zuwa yanzu, babu cikakken bayani kan halin da shugaban ƙasa da manyan jami’an gwamnati ke ciki, yayin da jama’a ke jiran karin bayani daga bangaren sojoji da kuma kungiyoyin ƙasa da ƙasa.

Cikakken bayani na nan tafe…

No comments