Wata ƙungiyar mai zaman kan ta da ke aiki a ƙarƙashin sunan 'Concerned Kaduna Citizens' (CKC) ta yi tir da kalaman tsohon gwamnan Ji...
Wata ƙungiyar mai zaman kan ta da ke aiki a ƙarƙashin sunan 'Concerned Kaduna Citizens' (CKC) ta yi tir da kalaman tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-rufai, bisa iƙirarin da ya yi cewa gwamnatin Gwamna Uba Sani ta biya Naira Biliyan Ɗaya ga ‘yan bindiga.Ƙungiyar ta bayyana zargin a matsayin ƙarya, yunƙurin karkatar da hankulan al'umma, kuma mai ɗaukewar siyasa.
Shugaban ƙungiyar, Abdulrashid Teslim, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a sakatariyar 'yan jarida NUJ a garin Kaduna, inda ya ce kalaman da El-rufai ya yi a hirar sa a gidan talbijin na Channels ba su da tushe ko kaɗan face neman bata sunan gwamnatin da ke kan mulki.
A cewarsa, babu wani lokaci da gwamnatin Jihar Kaduna ƙarƙashin Uba Sani ta taba biyan kuɗin fansa ko wani nau’in kuɗi ga ‘yan bindiga ko masu aikata laifuka.
Ya ce, yaɗa irin waɗannan labarai na iya janyo fargaba da ruɗani a zukatan jama’a, tare da iya jefa harkokin tsaro cikin haɗari.
Ƙungiyar ta jaddada cewa, gwamnatin Uba Sani ta rungumi tsari na rashin yin sulhu da masu laifi da kuma ƙin biyan kuɗin fansa, sai dai ta mayar da hankali kan amfani da hukumomin tsaro, bayanan sirri, da ƙoƙarin haɗa kai da al’umma domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya.
CKC ta ce, wannan tsari na gwamnati ya fara haifar da sakamako mai kyau a wasu sassan jihar, inda ake samun raguwar hare-haren ‘yan bindiga idan aka kwatanta da shekarun baya.
A wani bangare na martaninta, ƙungiyar ta kuma caccaki mulkin El-rufai, tana mai cewa a lokacin gwamnatinsa ne Kaduna ta fuskanci mafi muni na kashe-kashe, sace-sacen mutane da tashin hankali a tarihinta na baya-bayan nan.
Ƙungiyar ta kwatanta wannan da zamanin tsofaffin gwamnonin jihar Ahmed Makarfi, Namadi Sambo da Mukhtar Ramalan Yero, waɗanda suka ce mulkinsu ya samar da kwanciyar hankali da zaman lafiya, kuma wasu daga cikinsu har yanzu na bayar da gudunmawa a ƙoƙarin gina zaman lafiya a jihar.
Ƙungiyar ta buƙaci tsohon gwamnan da ya daina yin kalamai masu tayar da hankali ba tare da hujja ba, tare da kiran ‘yan siyasa da su rungumi gaskiya da maganganu masu tsafta domin kare zaman lafiyar al’umma.

No comments