Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

KEBBI: Ba Za Mu Yi Barci Ba Har Sai ’Ya’yan Ku Sun Dawo – Shettima Ga Iyayen Ɗaliban Maga

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa iyayen ɗalibai mata 25 da aka sace a Makarantar Sakarandaren Gwamnati ta Maga , Jihar Kebbi , cewa za ta y...



Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa iyayen ɗalibai mata 25 da aka sace a Makarantar Sakarandaren Gwamnati ta Maga, Jihar Kebbi, cewa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ceto su cikin ƙoshin lafiya.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya isa Birnin Kebbi a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce wannan mummunan lamari ya taba zuciyar kowane ɗan Nijeriya.



Ya ce Shugaba Tinubu “ya damu matuƙa” kuma yana jin zafin abin da ya faru a matsayinsa na uba nagari.

Shettima ya bayyana cewa sace ɗaliban matsayin hari ne ga lamiri da ɗabi’ar jama’ar Nijeriya, kana ya tabbatar da cewa za a yi amfani da dukkan hanyoyin gwamnati domin dawowa da yara da hukunta masu laifin da suka kashe Brigadier-General Musa Uba da sauran waɗanda aka hallaka.

Ya ce: “Raɗaɗin Kebbi raɗaɗin Nijeriya ne. Duk inda aka sace yaro, duk gidaje a ƙasar nan na cikin baƙin ciki. Shugaban Ƙasa ya damu ƙwarai. Wannan ba lokacin siyasa ba ne, lokaci ne na haɗin guiwa domin dawo da ‘ya’yanmu lafiya.”

Mataimakin Shugaban Ƙasa ya ƙara da cewa hawaye da tsoro da raɗaɗin iyayen waɗannan dalibai “tabo ne a kan lamirin Nijeriya,” kuma gwamnati ba za ta yi sakaci da alhakin ta ba.

Ya kuma mika saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayi Brigadier-General Musa Uba da sauran jami’an tsaro da suka rasa rayuka, yana mai cewa ƙasar ba za ta manta da sadaukarwarsu ba.

Shettima ya yaba wa Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris, da shugabanni na al’umma da masu tsaron gida, bisa yadda suka haɗa kai domin kare yankin da kuma tallafawa binciken gano ‘yan matan.

A nasa jawabin, Gwamnan Kebbi ya gode wa Shugaban Ƙasa bisa kulawa da jagoranci, yana mai tabbatar da cewa da irin jajircewar da ake yi yanzu, akwai kyakkyawan fata cewa za a ceto ɗaliban cikin gaggawa.


No comments