Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ina Nan Daram A Jam'iyyar APC -Bello Bakyasuwa

  Daga Hussaini Yero, Gusau Tsohon Darakta a Ma'ikatar tsaro ta Jihar Zamfara, kuma tsohon Kwammanda na Hukumar Hana Ta'addanci da k...


  Daga Hussaini Yero, Gusau

Tsohon Darakta a Ma'ikatar tsaro ta Jihar Zamfara, kuma tsohon Kwammanda na Hukumar Hana Ta'addanci da kuma Bangar Siyasa, Kuma tsohon Sakataren yaɗa labarai na tsohuwar tafiyar Jam'iyyar APC Bangaren Senata Kabiru Garba Marafa, Muhammad Bello Bakyasuwa ya bayyana cewa tana nan daram a Jam'iyyar APC ƙarƙashin Jagorancin Ministan tsaro, Bello Muhammad Matawallen Maradun da Sanata Abdul'aziz Yari, domin shi santsi bai kwashe shi ba.

Muhammad Bakyasuwa ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya sa ma hannu ga manema labarai a Gusau

Ya ce, "Ina sheda wa al'umar jihar Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya cewa, ban fita daga Jam'iyya ta ta APC ba, ina nan Daram. Dalili na na ƙin ficewa daga Jam'iyyar APC shi ne, kowa ya sani cewa Ita ce Jam'iyya mafi ƙarfi da yawan al'uma a Jihar Zamfara da ma ƙasa baki ɗya. 

Kuma idan muka lura, ƙarfin Jam'iyyar APC kullum ƙaruwa ta ke yi a Jihar Zamfara. Jam'iyyar mu ta APC ita ke da rinjaye a faɗin Jihar Zamfara da Nijeriya.

Don haka sai Bello ya ce shi da Magoya baya sa gaba ɗaya suna nan a Jam'iyyar APC, ƙarƙashin Jagorancin Ministan Tsaro Hon. Bello Matawalle da Jagora Tsohon Gwamna Sanata Abdul'aziz Yari Abubakar. 

Ya ce, "Ni Bakyasuwa Na zabi in ci gaba da biyayya ta siyasa ƙarƙashin Maigirma Minista, Hon. Bello Matawalle da kuma Sanata Abdul'aziz Yari Abubakar.

"Za mu yi aiki tsakanin mu da Allah domin nasar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu mu ga cewa ya lashe zaben Shugaban ƙasa a shekarar 2027  in sha Allah. 

Bakyasuwa ya kuma bayyana cewa, "Ina amfani da wannan dama in yaba wa,l Hon. Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu (Dan MajalisarTarayya Mai Wakiltar Mazabar Tarayya ta Bungudu da Maru), da kuma Hon. Yazid Shehu Danfulani akan Jajircewar su domin gina APC da kuma nema wa Jam'iyyar Al'umma."

No comments