Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Kaduna Ta Ayyana Asabar Ta Ƙarshen Kowane Wata A Matsayin Ranar Tsaftar Muhalli

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ayyana Asabar ta ƙarshen kowane wata a matsayin Ranar Tsaftar Muhalli ta Jiha, wani mataki da ta ce za a yi amfani...

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ayyana Asabar ta ƙarshen kowane wata a matsayin Ranar Tsaftar Muhalli ta Jiha, wani mataki da ta ce za a yi amfani da shi wajen ƙarfafa tsafta, kare lafiyar jama’a da kuma rage barazanar da ke fitowa daga rashin tsafta a faɗin jihar.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ahmed Maiyaki, ya fitar, an bayyana cewa aikin tsaftar na farko zai gudana ne a Asabar, 29 ga Nuwamba, 2025, daga ƙarfe 7:00 na safe zuwa 10:00 na safe.

A nasa jawabin, Kwamishinan Muhalli na jihar, Abubakar Buba, ya bayyana wannan shiri a matsayin wani gagarumin mataki na samar da ƙauyuka da birane masu tsafta, aminci da ingantacciyar lafiya. Ya yi kira ga shugabannin al’umma, ƙananan hukumomi, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye wajen shajja'a jama’a su fito su ba da tasu gudunmawar.

“Ana samun jiha mai tsafta ne idan al’ummarta sun farka sun ɗauki nauyin muhallinsu. Muna kira ga kowane mazaunin Kaduna ya fito ya ba da gudunmawa,” inji Buba.

Ya ƙara da cewa, gwamnati za ta tura ƙungiyoyin sa ido na musamman zuwa sassa daban-daban na jihar domin tabbatar da bin doka da ingantaccen tafiyar da shirin.

Haka nan, Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ahmed Maiyaki, ya jaddada cewa shirin tsaftar muhalli na daga cikin manyan manufofin Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, na rage ambaliya, hana yaɗuwar cututtuka da kuma kare lafiyar jama’a.

“Wannan ba batun share titi kawai ba ne; tsari ne na rigakafi don daƙile ambaliyar ruwa, rage haɗarin muhalli da kuma tabbatar da lafiyar al’ummar Kaduna,” in ji shi.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi kira ga al’umma da su mara wa wannan shiri baya gaba ɗaya, tana mai jaddada cewa tsaftar muhalli nauyin kowa da kowa ne, kuma ginshiƙi ne na rayuwa mai lafiya da ɗorewa.
 

No comments