Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shariff Sale Ne Zai Jagoranci Sallar Jana'izar Sheikh Dahiru Usman A Stadium

Daga Khalid Idris Doya  Dubban ɗaruruwan al'ummar Musulmai za su hallara gobe Juma'a da misalin karfe 3 na rana (3pm) a filin wasann...


Daga Khalid Idris Doya 

Dubban ɗaruruwan al'ummar Musulmai za su hallara gobe Juma'a da misalin karfe 3 na rana (3pm) a filin wasanni na Abubakar Tafawa Balewa Stadium da ke Bauchi domin gudanar da sallar jana'izar fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda ya rasu a ranar Alhamis. 

Za a gudanar da jana'izar ne a babban filin taro na Tafawa Balewa Stadium Bauchi da ke cikin kwayar Bauchi. 

Babban aminin marigayin, Shariff Ibrahim Saley Al'husainiy, shi ne zai jagoranci sallar jana'izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Ana sa ran jama'a daga sassa daban daban na Afrika ne za su halarci wannan jana'izar. 

A sanarwar da ta fito daga gidan marigayi Sheikh Dahiru Usman, wanda M Daha Azhary Bauchi ya fitar ya shaida cewar, "Jana'izar Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi..... Babban Amininsa Shariff Ibrahim Saley Al'husainiy, shi ne zai Jagoranci yi masa Sallah kamar yadda yyi Wasiyya.

"Za a yi Sallar ne a Gobe Juma'a 28-11-2025 a babban filin taro na Tafawa Balewa Sports Stadium Bauchi da ƙarfe 3:00 wato bayan Sallar Juma'a," in ji M Daha Azhary Bauchi.
 

No comments