Daga Zubairu M Lawal Lafia Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, a ranar Laraba ya gabatar da kasafin kuɗin shekara ta 2026 mai ...
Daga Zubairu M Lawal Lafia
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, a ranar Laraba ya gabatar da kasafin kuɗin shekara ta 2026 mai kimanin Naira Biliyon 517.5 ga Majalisar Dokokin jihar domin amincewa.
Yayin da yake gabatar da kasafin da aka kira “Kasafin Haɓakar Ci gaba” a dakin majalisar da ke garin Lafia, Gwamna Sule ya gode wa ’yan majalisar bisa goyon bayan da suke ba shi wajen amincewa da kasafin kuɗi a koyaushe.
Ya bayyana cewa taken kasafin kuɗin na 2026 ya dace da manufofin gwamnatinsa na ci gaba da ayyukan gina masana’antu, haɓaka haɗin kan manyan ayyuka da inganta tattalin arziki.
A cewar gwamnan, an ware Naira Biliyon 212.79 adadin (41.12%) don kashe-kashe na yau da kullum, yayin da N304.75 biliyan za a kashe su kan manyan ayyukan raya kasa.
Sule ya ce rabon kuɗin da aka ware ga ayyukan yau da kullum da na manyan ayyuka ya nuna jajircewar gwamnatinsa wajen zuba jari a abubuwan ci gaba na dogon lokaci.
Rarraba kasafin kuɗi ta fannonin gwamnati:
Bangaren Gudanarwa zai lashe N108.70bn
Bangaren Tattalin Arziki ya samu N221.84bn
Bangaren Dokoki da Shari’a: N16.09bn
Bangaren Zamantakewa: N170.92bn
Ayyukan Gine-gine: N157.80bn (30.5%)
Bangaren Ilimi: N92.91bn (7.95%)
Kimiyya, Fasaha da Tattalin Arzikin Dijital: N4.92bn (0.95%)
Bangaren , Tsaro da Gudanarwa: N142.96bn (27.62%)
Kudi, Zuba Jari da Kasuwanci: N39.19bn (7.57%)
Lafiya: N37.19bn (7.19%)
Noma da Ruwan sha N31.85bn (6.15%)
Muhalli da Cigaban Al’umma: N28.32bn (5.42%)
Bayar da Bayanai da yawon bude ido: N18.65bn (3.60%)
Majalisa: N16.59bn (3.21%)
Fannin Shari’a: N16.09bn (3.11%) Bangaren Matasa da Wasanni: N10.01bn (1.93%)
Jin Kai da Inganta Mata: N2.50bn (0.48%)
Gwamna Sule ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙari wajen gina ƙarfin gwamnati domin bauta wa jama’ar jihar Nasarawa yadda ya kamata.
Da yake karɓar kundin kasafin, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Dr. Danladi Jatau, ya tabbatar wa gwamnan cewa majalisar za ta yi aiki tare da shi kuma za ta hanzarta amincewa da kasafin kuɗin domin ci gaban jihar.
Ya kuma bukaci ma’aikatu da hukumomi su kiyaye ka’idojin kasafin kuɗi yayin aiwatar da shi.
Jatau ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da zaman lafiya, haɗin kai da mutunta juna ba tare da la’akari da bambancin siyasa, kabila ko addini ba.
A ƙarshe ya bukaci jama’a da su ci gaba da goyon bayan Gwamna Abdullahi Sule domin gina jihar Nasarawa mai cigaba.

No comments