Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Kebbi Ya Zargi Jami’an Tsaro Da Sakaci Kan Sace Ɗalibai A Maga

Gwamnan Jihar Kebbi, Mohammed Nasir Idris, ya nuna tsananin ɓacin ransa a daren Litinin kan abin da ya kira gazawar bin bayanan sirri da Huk...



Gwamnan Jihar Kebbi, Mohammed Nasir Idris, ya nuna tsananin ɓacin ransa a daren Litinin kan abin da ya kira gazawar bin bayanan sirri da Hukumar Tsaro ta DSS ta bayar, wanda ya nuna cewa akwai yiwuwar kai hari a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta ’Yan Mata, Maga, da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu.

A safiyar Litinin ne wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka farmaki makarantar, inda rahotanni suka ce sun kashe mataimakiyar shugaban makarantar kuma suka yi awon gaba da dalibai mata 25. Daga cikinsu, uku sun tsere da ransu.

Rahoton Pointblanknews.com ya ambato wata majiya mai tushe da cewa Gwamna Idris, wanda ya isa makarantar kusan ƙarfe 6:45 na yamma, ya yi zargin cewa wasu jami’an tsaro sun yi sakaci ko gurbata kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen tabbatar da tsaro.

Ya ce: “Wannan babban aiki ne na cin amanar gwamnati. Mun samu cikakken bayanan sirri daga DSS cewa za a iya kai wa wannan makarantar hari. DSS ta kuma ba da shawarar a kira gaggawar zaman Majalisar Tsaro, wanda muka yi. An yanke hukuncin samar wa makarantar kariya na ko wane lokaci.”

Gwamnan ya ce ya ɗauki rahoton DSS da matuƙar muhimmanci, yana mai tuna cewa irin wannan gazawar bin bayanan sirri ce ta haifar da sace dalibai sama da 300 a Kankara, jihar Katsina, a watan Disamba 2020.

Ya bayyana takaicinsa cewa duk da an tura jami’an tsaro don kare makarantar, sun bar wurin ba tare da wani bayani ba. A cewarsa, jami’an tsaron da aka tura sun dauki lokaci suna daukar hoto da dalibai, sannan suka bar su awanni kafin harin faruwa.

Gwamnan, tare da manyan shugabannin tsaro na jihar, ya sanar da kafa kwamitin bincike na musamman domin gano dalilin da ya sa duk da bayanan sirri da DSS ta bayar da matakan da gwamnati ta ɗauka, harin ya samu nasara.

Kwamitin, wanda zai kula da dawo da daliban da aka sace lafiya, zai kasance karkashin jagorancin Daraktan DSS na jihar.

Wani malamin makarantar da ya tsira ya bayyana mamakinsa, yana mai cewa ganin yawan jami’an tsaro da aka tura ranar Lahadi, har ma suna koyar da dalibai dabarun kare kai, bai yi tunanin abubuwan da suka faru ba.

A cewarsa: “Jami’an tsaron da suka zo sun kwana suna gadin makarantar. Amma abin bakin ciki shi ne, sun bar wurin da sassafe ba tare da wani dalili da aka sani ba. Kimanin mintuna 30 bayan barin su, sai ga ’yan bindigar sun afka suka sace daliban.”

Ya ce yana ganin sahihancin bayanan DSS ne ya sa Gwamna Idris ya naɗa daraktan hukumar kan kujerar shugaban kwamitin.

Malamin ya kara da cewa akwai kwarin gwiwa cewa an sace daliban ba a kashe su ba, tare da fatan cewa kokarin da Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kebbi ke yi zai taimaka wajen ceto su baki ɗaya.

No comments