Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bidiyon Saukar Kashim Shettima A Kebbi

   Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya isa Birnin Kebbi, inda yake jagorantar tawagar Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin umarnin Shugaban Ƙ...


 
 Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya isa Birnin Kebbi, inda yake jagorantar tawagar Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin umarnin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, don bibiyar halin da ake ciki kan aikin ceton ƴan matan da aka sace a makaranta kwana ta garin Maga.

A lokacin ziyarar, Mataimakin Shugaban Kasar zai yi ganawar sirri da gwamnan jahar don duba yadda aikin haɗin gwiwa ke gudana tsakanin gwamnatin jihar da ta tarayya kan yadda za a dawo da wadannan yan mata cikin gaggawa da aminci, inda a nan zai isar Isar da jajen Shugaban Kasa ga jihar kan matsalolin tsaro da suka yi ƙamari a kwanakin nan, tare da ƙarfafa shirin gwamnati na bai wa makarantu tsaro da kare haƙƙin kowane yaro na samun ilimi a faɗin ƙasar nan.

 Har ila yau, Mataimakin Shugaban Kasa Shettima zai gudanar da wasu muhimman taruka da sarakunan gargajiya, shugabannin jami’an tsaro, da iyayen ɗaliban da aka sace karkashin jagorancin gwamnan jahar Kebbi, Nasir Idris don duba yadda ake ci gaba da ƙoƙarin ceto yaran a matakai daban-daban.

Ita dai tawagar ta Mataimakin Shugaban Kasa ta ƙunshi manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki da suka haďa da Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na Ƙasa, da Dr. Bernard Doro, Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Hon sai Imaan Sulaiman-Ibrahim, Ministar Harkokin Mata da Hajiya Zubaida Umar, Darakta-Janar ta Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA).
Mutanen da tawagar ta kunsa na nuni da yadda gwamnatin tarayya ta dauki lamarin da muhimmanci inda tuni Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dakatar da duka tafiye-tafiyensa don bibiyar yadda za a shawo kan lamarin.

No comments