Rikici ya barke a harabar Kotun Majistare ta Kuje bayan jami’an ‘yan sanda sun sake kama ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan adam kuma tsohon...
Rikici ya barke a harabar Kotun Majistare ta Kuje bayan jami’an ‘yan sanda sun sake kama ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, mintuna kaɗan bayan an ba shi beli.
Shaidu sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan alkalin kotun ya bayar da belin Sowore da wasu mutum 13 da aka gurfanar.
Rahotanni daga Sahara Reporters sun nuna cewa yayin da lauyoyinsa ke kammala shirin cika sharuddan belinsa, jami’an ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin CSP Ilyasu Barau, wanda shi ne jami’in bincike (IPO) kuma shugaban sashen Anti-Vice na DC-CID, FCT Command, sun kai masa hari, suka doke shi sannan suka tilasta shi shiga mota.
Wani shaida ya bayyana cewa Sowore ya yi ƙoƙarin hana jami’an ɗaukar sa saboda ba su bayyana dalilin kama shi ba.
“IPO ɗin ya buge shi, ya ja shi ƙasa, sannan ya tilasta shi shiga motar ‘yan sanda. Sun yi masa mummunan duka,” in ji shaidar.
Wani majiyar ma ta ƙara da cewa:
“Da muka tambayi jami’an ko suna da umarnin sake tsare shi daga kotu, sai suka ƙi nuna wata takarda. Sun ce suna da umarni na sirri daga wata babbar kotu don kai shi gidan yari na Kuje.”
Rahotanni sun ce an tafi da Sowore zuwa gidan gyaran hali na Kuje duk da cewa kotu ta bayar da belinsa, abin da ya haifar da cece-kuce a tsakanin ‘yan jarida, lauyoyi da masu fafutuka da suka halarci zaman kotun.

No comments