Hedkwatar Sojojin Sama na Nijeriya (NAF) ta sanar da fitar da sunayen masu nema da aka tantance domin shiga jarrabawar 'Zonal General Ap...
Hedkwatar Sojojin Sama na Nijeriya (NAF) ta sanar da fitar da sunayen masu nema da aka tantance domin shiga jarrabawar 'Zonal General Aptitude Test' ta shirin ɗaukar ma’aikata na 'Direct Short Service Commission' (DSSC) 34/2025.
A sanarwar da kakakin rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar, NAF ta bayyana cewa jarrabawar za a gudanar da ita ne a Asabar, 25 ga Oktoba 2025, a cibiyoyi daban-daban a faɗin ƙasar.
Masu nema da suka cancanta an bukace su su duba shafin yanar gizon NAF — https://nafrecruitment.airforce.mil.ng — domin ganin cikakkun bayanai da kuma wurin jarabawa da aka ware musu.
Rundunar ta kuma ja hankalin wadanda abin ya shafa da su isa cibiyoyinsu na jarabawa da wuri kamar yadda aka nuna a gaban sunayensu a shafin.

No comments