Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Sauke Hafsoshin Tsaro, Ya Maye Gurbin Su

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sauke Janar Christopher Musa daga muƙaminsa na Babban Hafsan Tsaron Kasa, da sauran hafsoshin tsaro na k...



Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sauke Janar Christopher Musa daga muƙaminsa na Babban Hafsan Tsaron Kasa, da sauran hafsoshin tsaro na kasa baki ɗaya.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sunday Dare, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, ya fitar a ranar Jumma’a.

A cewar sanarwar, an nada Janar Olufemi Oluyede, wanda shi ne Shugaban Sojin Ƙasa, a matsayin Sabon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa.

An kuma naɗa Manjo Janar W. Shaibu a matsayin Shugaban Sojin Ƙasa, Air Vice Marshal S.K. Aneke a matsayin Shugaban Rundunar Sojin Sama, da Rear Admiral I. Abbas a matsayin Shugaban Rundunar Sojin Ruwa.

Manjo Janar E.A.P. Undiendeye, wanda shi ne Shugaban Sashen Leken Asirin Tsaro (Defence Intelligence), zai ci gaba da rike mukaminsa.

Sanarwar ta bayyana cewa wannan sauyi na cikin shirin gwamnati na inganta tsaron a Nujeriya.

Shugaba Tinubu, ya gode wa tsohon Babban Hafsan Tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa, da sauran tsoffin hafsoshi bisa gudunmawa da jagorancin da suka yi.

Ya kuma buƙaci sabbin hafsoshin da su nuna ƙwarewa, jajircewa, da haɗin kai domin inganta tsaro a Nijeriya.

No comments