Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NEMA Ta Yaba Da Gudumawar NAF Wajen Kare Rayuka A Arewa Maso Gabas

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta yaba da gudumawar Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF), ta hanyar ba ta lambar yabo ta ƙware...


Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta yaba da gudumawar Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF), ta hanyar ba ta lambar yabo ta ƙwarewa bisa jajircewa da sadaukar da kai wajen bayar da taimakon jin ƙai da goyon bayan al’umma a Jihar Adamawa.

An gabatar da lambar yabo ga 153 Base Services Group da ke Yola ta hannun shugaban ofishin NEMA na Yola, Mista Ladan Ayuba, a ranar 15 ga Oktoba, 2025. A wajen taron, Mista Ayuba ya bayyana cewa rundunar ta nuna “ƙwazo da kishin ƙasa fiye da kima” tun daga shekarar 2014 zuwa yau.

Ya ce Sojin Sama sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da taimakon likitoci ga mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, da kuma lokacin ambaliyar ruwan da ta afka a Karamar Hukumar Yola ta Kudu a watan Yuli 2025.

“A lokutan tashin hankali da gaggawa, lokacin da rayuka ke cikin haɗari, Sojin Sama na 153 Base Services Group su ne ke farko wajen ɗaukar mataki — suna tura jami’ai, motocin ceto da ƙungiyoyin likitoci domin taimakon masu fama da bala’i,” inji Mista Ayuba.

Lambar yabo ta kuma haɗa da yaba wa rundunar bisa taimako wajen jigilar masu buƙatar ceto, samar da ruwan sha ga sansanonin ’yan gudun hijira, bayar da tsaro yayin raba kayan tallafi da taimakawa wajen dawo da jama’a zuwa gidajensu cikin aminci.

Shugaban rundunar 153 Base Services Group, Group Captain Mu’azu Mohammed Mu’azu, shi ne ya karɓi lambar yabo a madadin Rundunar Sojin Sama. Ya miƙa godiya ga Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hasan Bala Abubakar, da kuma Air Vice Marshal Patrick Obeya bisa jagoranci da kulawa.

“Wannan yabo shaida ce ta hangen nesa da jajircewar shugabancin rundunar Sojin Sama, tare da sadaukar da kowane jami’i wajen kare rayuka da tallafawa al’umma,” inji Mu’azu.

Wannan karramawa ta yi daidai da hangen nesa na Babban Hafsan Sojin Sama wajen gina Rundunar Sojin Sama mai mayar da hankali kan jama’a, tare da ƙarfafa rawar da rundunar ke takawa wajen ci gaban ƙasa da taimakon jinƙai.q








 

No comments