Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Sake Kunno Kai, Makiyaya Sun Sare Hannun Manomi A Borno

Wani hari mai tsanani da ake zargin Fulani makiyaya ne suka kai ya jikkata wani manomi mai suna Mohammad Ali Fantami, a ƙauyen Jakana, ƙaram...



Wani hari mai tsanani da ake zargin Fulani makiyaya ne suka kai ya jikkata wani manomi mai suna Mohammad Ali Fantami, a ƙauyen Jakana, ƙaramar hukumar Konduga ta jihar Borno.

Rahotanni daga mai nazarin tsaro, Zagazola Makama, sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, lokacin da wasu makiyaya suka shigar da shanunsu cikin gonar wake mallakin mazauna yankin, suka bar su suna cin amfanin gona.

A cewar Makama, Fantamin, wanda ke da shekaru 30, ya yi ƙoƙarin korar shanun daga gonarsa, sai ɗaya daga cikin makiyayan ya kai masa hari da adda.

“Mai harin ya sare masa hannun hagu gaba ɗaya, sannan ya yi masa mummunan rauni a wuya kafin ya tsere,” inji Makama.

An garzaya da wanda abin ya faru da shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), inda yake karɓar magani a halin yanzu.

Rahoton ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da bincike don kamo waɗanda suka aikata wannan aika-aika.

A cikin ‘yan shekarun nan, hare-haren da ke tsakanin manoma da makiyaya sun addabi sassa da dama na Nijeriya. A shekarar 2019, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da shirin RUGA (Rural Grazing Area) domin warware rikicin, amma aka ƙi karɓa musamman a yankunan kudu na ƙasar.

No comments