Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ba Zan Haɗa Kai Na Matsayi Ɗaya Da Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

Daga Khalid Idris Doya  Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya amince da naɗa babban yayansa, Alhaji Adamu Muhammad Duguri a matsayin Sarkin...


Daga Khalid Idris Doya 

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya amince da naɗa babban yayansa, Alhaji Adamu Muhammad Duguri a matsayin Sarkin sabuwar masarautar Duguri, a matsayin Sarki mai daraja ta 1.

Da ya ke jawabi bayan amsar wasiƙar zama sabon sarkin wanda tawagar gwamnatin jihar suka miƙa mishi a ranar Juma'a, mai martaba Sarkin Duguri, Alhaji Adamu, ya tabbatar da cewa zai haɗa kai da sauran sarakunan jihar Bauchi domin kawo ci gaba ga al'umma.

Ya jaddada cewa zai yi biyayya ga manyan sarakunan jihar da suka gabace shi musamman Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu domin ganin an samu kyakkyawar yanayin jagoranci na kwarai da wanzar da zaman lafiya.

"Ina tabbatar da cewa manyan sarakunan da suke yi kafin zuwanmu za mu zauna da su lafiya, za mu zauna cikin ladabi da biyayya, ba za mu janyo wani fitini da zai kawo rikici ba," ya tabbatar.

Sarki Adamu wanda tsohon jami'in Kwastam da ya kammala aiki a matsayin mataimakin Kwanturola ya tabbatar da cewa zai yi biyayya wa gwamnati da dokoki domin kyautata rayuwa tare da cewa sarakuna suna da gagarumin rawar da suke takawa wajen kawo cigaba a cikin al'umma.

Ya ce ɓangaren ilimi aiki ne sosai da zai tabbatar ya bayar da gudunmawarsa domin ganin yara suna koma zuwa makaranta yadda ya kamata.

Har-ila-yau, ya kuma nanata aniyarsa na mara wa gwamnati baya a ɓangaren inganta kiwon lafiya da tsaro. 

Sarkin Duguri wanda shi ne shugaban hukumar kula da ilimi a matakin farko (SUBEB) a jihar Bauchi ya nuna farin cikinsa da godiyarsa ga Allah bisa wannan damar da ya samu, ya kuma gode wa gwamnan jihar Bala Muhammad bisa naɗa shi da ya yi tare ba da tabbacin yin aiki tuƙuru domin ci gaban al'ummarsa da ma jihar Bauchi baki ɗaya.

Ya hori al'ummar masarautarsa da su haɗa kai tare da bayar da nasu gudunmawar wajen kawo ci gaba da kowa zai amfana.

"Mu mutanen Duguri a shirye muke, duk wani abun da gwamanti ta ce a yi a shirye muke mu yi. A shirye muke mu kai yara makaranta, a shirye muke in kawo riga-kafi mu yi. 

"Muna zaune lafiya tare da makwabtanmu. Mu godiya sosai wa mai girma Gwamnan. Bisa tabbatar da wannan lamarin wanda al'ummar Duguri suka jima suna neman," Sarkin ya tabbatar. 

Daga bisani ya sanar da bai wa Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad sarautar 'Yariman Duguri' a matsayinsa na ɗan masarautar kuma gwarzo a garesu.

Da ya ke miƙa mishi takardar zama Sarki, Sakataren Gwamanti jihar Bauchi, Aminu Hammayo ya ce gwamnan jihar Bala Muhammad ya yi amfani da dokar masarautu ta jihar Bauchi na shekarar 2025 musamman sashi na 16 da 17 da shawarwari da hukumomin da suke kula da zañan sarakuna da kuma kula da al'adu ya naɗa Alhaji Adamu Mohammed Duguri 'Sarkin yanka' mai daraja ta 1 a masarautar Duguri.

SSG ya miƙa sakon gwamnan jihar wa sabon Sarkin ta hanyar tunatar da shi cewa ya tafiyar da harkokin masarautar kan bin kundin tsarin mulkin ƙasa, dokokin jihar Bauchi da umurni da ƙa'idoji da lokaci zuwa lokaci zai ke fitowa daga wajen gwamnati da cewa ya kula da waɗannan a kowani lokaci wajen gudanar da harkokin mulkin masarautar. 

Ya kuma horeshi da ya wanzar da gaskiya da adalci a yayin da yake jagorantar al'ummar Masarautar Duguri.  Gwamnan ya yi fatan za a samu ƙarin zaman lafiya da haɗin kai, ƙarin arziki a ƙarƙashin jagorancin sabon Sarkin.
 

No comments