Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NULGE, NUT Sun Yabi Gwamnan Kaduna Bisa Amincewa Da Sabon Albashi Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi

...Sun Dakatar Da Yajin Aikin Gargadi Ƙungiyoyi Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi na Nijeriya (NULGE) da ƙungiyar Malamai ta Nijeriya (NUT), da ƙu...


...Sun Dakatar Da Yajin Aikin Gargadi

Ƙungiyoyi Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi na Nijeriya (NULGE) da ƙungiyar Malamai ta Nijeriya (NUT), da ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Nijeriya (MHWUN) sun yaba wa Gwamna Uba Sani bisa amincewa da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa, tare da ƙarin albashi ga dukkan ma’aikatan Ƙananan Hukumomi.

A wani taron manema labarai da suka gudanar a Kaduna, shugabannin ƙungiyoyin, Kwamared Rayyanu Isyaku Turunku na (NULGE), Kwamared Ibrahim Dalhatu na (NUT) da Kwamared Umar Ibrahim Fatika na (MHWUN) duk sun bayyana matakin gwamnan a matsayin nuna tausayawa, adalci da jajircewa wajen kare jin daɗin ma’aikata.

Hakazalika, Sun sanar da dakatar da yajin aikin gargadi da suka shirya, bayan gwamnan ya amince da aiwatar da sabon tsarin albashi ga dukkan ma’aikatan kananan hukumomi, ciki har da ma’aikatan da ke ƙarƙashin  hukumar ( SUBEB) da Hukumar Kula da Lafiyar  a matakin Farko (Primary Healthcare Board), daga watan Oktoba, 2025.

“Shirin gwamnan na aiwatar da sabon tsarin albashi duk da ƙalubalen tattalin arziki ya nuna tausayinsa, gaskiya, da girmama kimar ma’aikata,” in ji shugabannin kungiyoyin.

Kungiyoyin sun kuma yaba da kokarin gwamnatin wajen gyara da inganta fannonin ilimi da kiwon lafiya inda suka  bayyana  gyaran da sabunta azuzuwan karatu a dukkan kananan hukumomi 23, amincewa da tsarin ritaya bayan shekaru 65 ko shekaru 40 na aiki ga malamai, da kuma dawo da sama da naira miliyan 500 na ajiyar ( ENDWELL) da aka rike a baya, a matsayin muhimman nasarori.

Ma’aikatan sun kara jinjina wa dawowar tsarin biyan gudunmawar  adashin gata na malaman makaranta wato  (ENDWELL) na kowane wata, inda suka bayyana cewa tsarin yana taimakawa wajen inganta walwalar malamai da iyalansu. Haka kuma sun yaba da gyaran da gwamnati ta yi wajen biyan kudin kungiyoyi  da kuma nasarar tantance ma’aikata wanda ya kara gaskiya da tsari a cikin aikin gwamnati.

A fannin lafiya, ƙungiyoyin sun yaba da sauye-sauyen da Gwamna Uba Sani ya aiwatar, ciki har da farfado da cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda 255 (PHCs), kafa cibiyoyin kwarewa guda 23 na PHC, da kuma shirin daukar ma’aikatan lafiya 1,800 a duk shekara na tsawon shekaru biyar.

Haka kuma shugabannin ma’aikatan sun jinjina wa gwamnan bisa kaddamar da motocin  bas masu aiki da iskar gas  (CNG) guda 100 domin bayar da kyautar sufuri ga ma’aikata da dalibai, suna bayyana wannan shiri a matsayin wani mataki na taimakawa wajen rage radadin cire tallafin mai da sauƙaƙa rayuwar jama’a.


 

No comments