Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Taya Sanata Kwankwaso Murnar Zagayowar Ranar Haihuwa

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon gwamnan jihar Kano, kuma shahararren ɗan siyasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar zagayow...


Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon gwamnan jihar Kano, kuma shahararren ɗan siyasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwar sa, wacce ta kasance yau, 21 ga Oktoba, 2025.

Shugaban ya taya 'yan uwa da abokan arzikin Kwankwaso da ma tawagar siyasar sa murna a yayin da suke bikin wannan rana mai muhimmanci.

Shugaban ya ce duba da irin gagarumar gudumawa da Kwankwaso ya bai wa ƙasar nan a dukkan muƙaman shugabanci daban-daban da ya riƙe, kama daga matsayin sa na tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai a Jamhuriya ta Uku da aka dakatar, sannan Gwamnan Jihar Kano na wa’adi biyu, kana Ministan Tsaro, da kuma Sanata mai wakiltar Yankin Kano ta Tsakiya, Kwankwaso ya bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban ƙasa.

Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa ƙarin haɓakar tasirin Sanatan a Arewacin Nijeriya, musamman a Jihar Kano, na da nasava da irin salon siyasarsa da ke bai wa muradun al’umma fifiko, wanda tayi kama da salon siyasar marigayi Mallam Aminu Kano da marigayi Alhaji Abubakar Rimi.

"Sanata Kwankwaso yana nan a matsayin aboki kuma takwaran aikina tun muna yan majalisar tarayya a 1992 sannan a matsayin gwamnoni a 1999"

"Har ila yau, mun yi aiki tare a yayin gwagwarmayar kafa Jam'iyyar All Progressives Congress (APC). Duk da cewa daga baya ya bar APC don kafa tasa Jam’iyyar ta New Nigeria Peoples Party (NNPP), amma abu mafi muhimmanci shine kasancewarsa jagora a sahun gaba a bangaren siyasa,”

Shugaban ya yi wa Kwankwaso fatan alheri, ɗorewar lafiya, da kuma karin shekaru masu amfani cikin hidimar al’umma.

No comments