Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Jihar Kaduna, Tare Da Haɗin Gwiwar AUDA–NEPAD Ta Tallafa Wa Ƙananan Manoma 400

Gwamnatin Jihar Kaduna, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ci gaban Afirka ta Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AUDA–NEPAD) reshen Nijeriya, ta ƙaddamar d...


Gwamnatin Jihar Kaduna, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ci gaban Afirka ta Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AUDA–NEPAD) reshen Nijeriya, ta ƙaddamar da rabon kayan noma ga kimanin ƙananan manoma 400 a faɗin jihar.

Gwamna Uba Sani ya sake tabbatar da kuɗirin gwamnatinsa na tallafa wa Ƙananan manoma da kuma ƙarfafa yawan amfanin gona a duk faɗin jihar, inda ya jaddada cewa noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin jihar.

A wani taron da aka gudanar a a gidan tatihi na Arewa House da ke Kaduna Gwamna Sani ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwa na nuni da yadda gwamnatin sa ke mai da hankali kan ci gaban da ya shafi jama’a kai tsaye, tare da daidaita gina tattalin arzikin da kuma samar da  wadataccen abinci, ɗorewa, da haɗin kai.

“Manoma ƙanana su ne ginshiƙin tsarin noman  mu sabida haka  tallafa musu yana nufin ƙarfafa tattalin arziki, tabbatar da wadatar abinci, da kuma inganta rayuwar dubban iyalai.”

Gwamnan ya bayyana cewa a ƙarƙashin shugabancin sa, noma yana ci gaba da kasancewa a sahun gaba na ayyukan gwamnati, inda aka ware fiye da Naira Biliyan 10 domin bangaren noma a kasafin kuɗin shekarar 2025.

Ya ƙara da cewa Kaduna ita ce jihar da ta cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa a yarjejeniyar Malabo kan saka hannun jari a harkar noma.

Shugaban AUDA–NEPAD a Nijeriya, Honarabul Jabir Abdullahi Tsauni, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa samar da kuɗaɗen haɗin gwiwa da suka bai wa shirin damar faɗaɗa zuwa dukkan Ƙananan Hukumomi 23 na jihar.

A cewar Tsauni, an horar da manoma ƙanana 345 kan kyawawan hanyoyin noma da kuma dabarun noma masu jituwa da yanayin sauyin yanayi, ciki har da noman lambu na gida irin su tumatir, barkono mai zaƙi, masara, wake, da waken soya. “Waɗannan kayan noma ba kayan aiki kawai ba ne, kayan fata da haɓaka tattalin arziki ne,” in ji shi.

Wannan shiri ya yi daidai da manufar “Renewed Hope” na  Shugaba Bola Tinubu da kuma Ajandar 2063 ta Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wacce ke mai da hankali kan noma mai haɗin kai da juriya ga canjin yanayi a matsayin tubalin ci gaban da ya dore.

Kwamishinan aikin gona na jihar Kaduna, Murtala Dabo, ya bayyana cewa wannan shiri ya nuna yadda jihar Kaduna ke da niyyar mayar da noma a matsayin sana’ar da ke kawo riba, ba kawai hanyar rayuwa ba.

Ya ce hakan na nuna irin jajircewar Gwamna Sani wajen tallafa wa haɗin gwiwa da ke kawo sauyin karkara, juriya ga sauyin yanayi, da tabbatar da wadatar abinci.

Dabo ya yaba wa AUDA–NEPAD bisa haɗin kai, tare da tabbatar da cewa Jihar Kaduna za ta ci gaba da kasancewa amintacciyar abokiyar hulɗa ga ƙungiyoyin ci gaba wajen haɓaka ƙirƙire-ƙirƙire a noma da tallafa wa manoma ƙanana.


 

No comments