Jam’iyyar AAC ta gudanar da babban taronta na jihar Kaduna a ranar Asabar, 18 ga Oktoba, 2025, a sakateriyar jam’iyyar da ke cikin birnin Ka...
Jam’iyyar AAC ta gudanar da babban taronta na jihar Kaduna a ranar Asabar, 18 ga Oktoba, 2025, a sakateriyar jam’iyyar da ke cikin birnin Kaduna, inda aka zaɓi sabbin jami’an gudanarwa domin tunkarar zaɓen 2027 da kuma ƙarfafa tsarin jam’iyyar a matakin jiha.
Taron, wanda ya kasance cike da natsuwa da haɗin kai, ya samu halartar Shugaban jam’iyyar na Kaduna, wanda kuma shi ne ya sake dawowa kan karaga, Hon. Musa Muhammad, da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa (reshen Arewa), Hon. Abdullahi Usman, tare da wakilai daga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) da kuma wakilan AAC daga sassa daban-daban na jihar.
A yayin taron, an tattauna kan hanyoyin da za su tabbatar da cewa jam’iyyar AAC ta tsaya da ƙafafunta sosai a jihar Kaduna kafin babban zaɓen 2027. Daga cikin manyan batutuwan da aka tattauna har da zaɓen sabbin jami’an gudanarwa bayan ƙarewar wa’adin su.
Wakilan jam’iyyar daga ƙananan hukumomi daban-daban sun amince da shugabannin jam'iyyar su ci gaba jagoranci cikin yardar juna, lamarin da ya nuna irin haɗin kan da ake samu tsakanin mambobin jam’iyyar a jihar.
A jawabin sa, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa (Arewa maso Yamma), Hon. Abdullahi Usman, ya jawo hankalin sabbin shugabannin da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da jajircewa. Ya kuma yi kira gare su da su zama masu kishin jam’iyya da bin doka da oda a duk ayyukansu.
Shi ma a nasa bangaren, Shugaban AAC na Jihar Kaduna, Hon. Musa Muhammad, ya yaba wa mambobin jam’iyyar bisa yadda suka gudanar da taron cikin kwanciyar hankali da haɗin kai. Ya kuma ƙarfafa wa shugabannin da su riƙe amana, su yi aiki tuƙuru domin ciyar da jam’iyyar gaba, yana mai cewa lokaci ya yi da AAC za ta zama abar koyi a fagen siyasa a jihar.
Sabon shugaban jam’iyyar ya kuma bayyana cewa, babban burin sabon shugabancin shi ne haɓaka jam’iyyar da kuma samar da zaƙaƙuran ‘yan takara da za su wakilci AAC a matakai daban-daban a zaɓen 2027. Ya roƙi mambobi da su haɗa kai wajen gina jam’iyyar mai ƙarfin gaske da za ta kawo sauyi mai ma’ana ga al’umma.
Jim kaɗan bayan kammala taron, yayin ganawa da manema labarai, Hon. Musa Muhammad ya bayyana cewa, jam’iyyar AAC ba ta da niyyar yin haɗaka da wata jam’iyya, domin manufarta ita ce ta ci gaba da tsaya da kafarta wajen ceto al’ummar ƙasa daga mawuyacin halin tattalin arziki da rashin gaskiya da suka dabaibaye shugabancin ƙasa.
Ya ƙara da cewa, “AAC jam’iyyar gaskiya ce, kuma za ta ci gaba da zama murya ta talakawa da masu rauni a cikin al’umma.”
Taron ya ƙare cikin annashuwa da fatan alheri, yayin da sabbin jami’an suka sha alwashin yin aiki tukuru don tabbatar da cewa AAC ta ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan jam’iyyun da za su taka rawa mai muhimmanci a siyasar jihar Kaduna da Nijeriya baki ɗaya.










No comments