Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hedikwatar Tsaro Ta Ƙaryata Jita-jitar Yunƙurin Juyin Mulki

Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta nesanta kanta daga wani rahoto da aka wallafa a kafar labarai ta yanar gizo, wanda ya danganta janye sha...


Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta nesanta kanta daga wani rahoto da aka wallafa a kafar labarai ta yanar gizo, wanda ya danganta janye shagulgulan bikin cikar Nijeriya shekara 65 da ’yanci da wani zargin yunƙurin juyin mulki da sojoji suka yi.

A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, rundunar ta bayyana cewa wannan labarin ƙarya ce tsantsa, wadda aka ƙirƙira domin tayar da hankalin jama’a da kuma ƙoƙarin kawo rashin amincewa ga jami’an tsaro.

Hedikwatar Tsaron ta bayyana cewa babu wani yunƙurin juyin mulki, kuma janye shagulgulan bikin cikar Nijeriya shekara 65 da ’yanci ya samo asali ne daga shirye-shiryen shugaban ƙasa na halartar wani muhimmiyar ganawa ta ƙasa da ƙasa, da kuma bukatar mayar da hankali kan yaƙin da ake yi da ta’addanci, ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a sassa daban-daban na ƙasar.

A cewar sanarwar, binciken da ake gudanarwa kan wasu jami’an soja 16 da aka kama ba ya da nasaba da siyasa ko yunƙurin juyin mulki, illa kawai horo ne na cikin gida da ke nufin tabbatar da ɗa’a da ƙwarewa a cikin rundunar soji.

“Kwamitin bincike na cikin gida an kafa shi yadda doka ta tanada, kuma sakamakon binciken zai zama a fili,” inji sanarwar DHQ.

Rundunar ta kuma roƙi ’yan ƙasa masu kishin ƙasa da su ci gaba da ba jami’an tsaro goyon baya wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar.

“Gwamnatin Tarayya, Majalisar Dokoki da kuma bangaren shari’a na aiki tare don tabbatar da tsaro, ci gaba da walwalar al’umma. Dimokuradiyya za ta ci gaba da wanzuwa,” inji DHQ.

A ƙarshe, rundunar ta gargadi jama’a da su yi watsi da labaran ƙarya da masu yaɗa jita-jita ke bazawa, tana mai jaddada cewa Sojojin Najeriya suna nan daram bisa biyayya ga tsarin mulki da kuma gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
 

No comments