Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NCDC Za Ta Yi Aiki Tare Da Gwamnoni Don Ci Gaban Yanki Arewa Ta Tsakiya - Shugaba

Daga Zubairu M Lawal Lafia  Shugaban Hukumar ci gaban yankin Arewa ta Tsakiya (NCDC), Kosmus Akighir, ya bayyana niyyar hukumar na yin aiki ...


Daga Zubairu M Lawal Lafia 

Shugaban Hukumar ci gaban yankin Arewa ta Tsakiya (NCDC), Kosmus Akighir, ya bayyana niyyar hukumar na yin aiki tare da gwamnonin jihohin domin gudanar da shirye-shiryen ci gaba a yankin.

Akighir ya bayyana hakan ne lokacin da mambobin hukumar suka kai ziyarar ban-girma ga Gwamnan Jihar Nasarawa a fadar gwamnati da ke Lafia, babban birnin jihar.

Ya ce hukumar za ta yi haɗin gwiwa da gwamnonin jihohi da sauran muhimman masu ruwa da tsaki a Arewa ta Tsakiya domin inganta rayuwar jama’a da kuma yaƙar talauci.

A cewar sa, goyon baya da haɗin kan gwamnonin jihohi na da matuƙar muhimmanci wajen cimma manufofin hukumar.

Akighir ya kuma yaba wa Gwamna Abdullahi Sule bisa irin ayyukan ci gaban da ya gudanar a jihar Nasarawa. Yana mai cewa yawancin ayyukan da aka kammala a Nasarawa na da alaƙa da manufofin hukumar.

A nasa jawabin, Gwamna Sule ya bayyana ziyarar a matsayin tarihi, domin ta nuna fara gudanar da ayyukan hukumar NCDC.

Ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewar sa wajen kafa hukumar, tare da gode wa sauran abokan aikin sa bisa goyon bayan da suka bayar wajen kafuwar hukumar, duk da cewa bai samu damar zuwa wajen taron ba.

Gwamna Sule ya kuma jaddada buƙatar gwamnatocin jihohi su tallafa wa hukumar ta fuskar kuɗi domin ta samu damar fara aiki yadda ya kamata.
 

No comments