Daga Hussaini Yero, Funtua 'Yan Jam'iyyar APC a jihar Zamfara a ƙarƙashin siyasar Sanata Kabiru Marafa sun bayyana goyan bayan su ...
Daga Hussaini Yero, Funtua
'Yan Jam'iyyar APC a jihar Zamfara a ƙarƙashin siyasar Sanata Kabiru Marafa sun bayyana goyan bayan su ga Tafiyar Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tunubu da Sanata Abdul'aziz Yari da Minista Bello Matawalle, inda suka Allah-wadai da ficewar sa daga Jam'iyyar.
Da yake jawabi a wajen taron da magoya bayan Sanata Marafa suka shirya a Gusau, tsohon Sakataren gudanarwa na ƙungiyar ta APC ta Marafa, Abdulƙadir Mijinyawa ya ce dubban magoya bayan APC a ƙarƙashin ƙungiyar tsohon Sanatan sun yi watsi da shawarar sa na ficewa daga APC.
Suka ce, “Saboda haka, a madadin dubban magoya bayan Marafa da ke faɗin Ƙananan Hukumomin jihar 14, ba mu bar jam’iyyar APC ba.
Ba mu gamsu da shawarar da Sanata Marafa ya yanke na barin jam’iyyar APC ba. Muna nan a APC, yanzu ba mu tare da shi siyasar Sanata Marafa."
A cewar Mijinyawa, su masu biyayya ga shugabancin APC a Zamfara ƙarƙashin Tukur Ɗanfulani.
Ya ce, “Kamar yadda kuke gani, wakilai daga magoya bayan jam’iyyar APC daga Ƙananan Hukumomi 14 da suka haɗa da dattawa, matasa da ƙungiyoyin mata da masu faɗa a ji na ƙungiyar siyasar Marafa suna nan.
"Muna goyon bayan Sen. Abdul'aziz Yari da ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle kuma za mu yi aiki domin samun nasarar Tinubu a zaben 2027," in ji shi.
Da yake mayar da martani, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Tukur Ɗanfulani, wanda Sakataren jam’iyyar, Ibrahim Ɗangaladima ya wakilta, ya yaba da matakin da magoya bayan jam’iyyar APC suka ɗauka na kin barin jam’iyyar APC.
Ɗanfulani ya ce: “Wannan abin farin ciki ne, ina godiya da ku, kun nuna kyakykyawan jajircewa don amfanin jam’iyyar APC A Zamfara da ƙasa baki daya.
“Kamar yadda muka sani, shugabancin jam’iyyar APC a jihar yana nan a dunƙule ya ke. Ina so in tabbatar muku da cewa jam’iyyar za ta ɗauki kowane ɗan jam’iyyar tare."
“Ina so in tabbatar muku cewa kowane ɗayanku za a yi masa daidai da matsayin ɗan jam’iyyar APC,” in ji Tukur Ɗanfulani.
No comments