Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa Hukumar Ilimin Fasahar Ƙere-ƙere ta Ƙasa (NBTE) bisa jajircewar ta ...
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa Hukumar Ilimin Fasahar Ƙere-ƙere ta Ƙasa (NBTE) bisa jajircewar ta wajen bunƙasa Ilimin Fasaha da Na Sana’o’i (TVET) a Nijeriya, musamman wajen kafa Cibiyar Ƙwarewa ta Sashen Ƙirƙira a Harkokin Watsa Labarai (Creative Media Sector Skills Council).
A wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, hadimin ministan na musamman kan harkokin yaɗa labarai ya fitar, ministan ya yi wannan yabo ne lokacin da Babban Sakataren NBTE, Farfesa Idris Bugaje, ya jagoranci membobin sabuwar cibiyar a ziyarar ban-girma zuwa ofishin sa a Abuja ranar Talata.
Ya ce: “Ina maraba da ku zuwa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai. Haka kuma, ina yaba wa NBTE bisa ƙoƙarin ta wajen bunƙasa Ilimin Fasaha da na Sana’o’i a Nijeriya, musamman ta hanyar Tsarin Ƙwarewar Ayyuka na Nijeriya.
"Na kuma yi farin ciki da ƙaddamar da Cibiyar Ƙwarewa ta Sashen Ƙirƙira a Harkokin Watsa Labarai, wadda ta ƙunshi manyan masu ruwa da tsaki daga ɓangaren gwamnati da na kamfanoni masu zaman kan su, don magance giɓin ƙwarewa a ɗaya daga cikin sassan tattalin arzikin mu da ke ta bunƙasa da canzawa.”
Ya bayyana cibiyar a matsayin tsarin da ke da gaskiya da adalci, wanda ke ƙarfafa masu aiki a fannin, tare da inganta abin da kafafen yaɗa labarai suke fitarwa.
Ya ƙara da cewa sashen ƙirƙira a harkar yaɗa labarai cike yake da mutane masu baiwa, amma sau da yawa ba ya da hanyoyin da aka tsara sosai domin gane ƙwarewa, da samun takardar shaidar ƙwarewa, da kuma daidaitawa da ƙa’idojin masana’antu.
Ya ce: “A gare mu a Ma’aikatar nan, tilas mu yi aiki da haɗin gwiwa. Ƙwararrun ma’aikatan kafafen yaɗa labarai da aka horar sosai kuma aka ba su takardar shaidar ƙwarewa za su iya inganta abubuwan da muke watsawa, su ƙarfafa ilimin kafafen yaɗa labarai, su yaƙi yaɗuwar labaran ƙarya, sannan su inganta martabar Nijeriya a cikin gida da waje.
"Aikin da kuke yi, kai-tsaye yana tallafa wa manufar mu ta tabbatar da yaɗuwar sahihan labarai masu bin ƙa’ida da ƙwarewa.”
Ministan ya tabbatar wa da NBTE da cibiyar cewa ma’aikatar sa za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da su wajen tsara hanyoyin da za a bi a haɗa da ƙa’idojin ayyuka ga jama'a na zamani, ɗaukar hoto, da shirya finafinai a harkokin yaɗa labarai da watsa shirye-shirye.
Ya jaddada cewa wannan shiri ya yi daidai da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Ya ce: “Cigaban fasaha da ƙwarewa suna cikin manyan ginshiƙai takwas na Ajandar Sabunta Fata, kuma ana ganin tasirin hakan bisa abin da NBTE ke aiwatarwa tare da sauran hukumomin gwamnati.”
Ya ambaci Asusun Lamunin Ilimi na Ƙasa (NELFUND) a matsayin ɗaya daga cikin shirye-shiryen gwamnati da ke tallafa wa ɗaliban Nijeriya.
A nasa jawabin, Farfesa Bugaje ya jaddada muhimmancin Tsarin Gano Ƙwarewar da Aka Samu Tun a Da (RPL), wadda za ta bai wa ƙwararrun da aka horar ba bisa tsari na hukuma ba, kamar ɗaliban koyon sana’a a fannin kafafen yaɗa labarai da watsa shirye-shirye damar samun takardar shaidar ƙwarewa ta ƙasa.
A nata tsokacin, Hajiya Fatima ta ce, “Cibiyar Ƙwarewa ta Sashen Ƙirƙire-ƙirƙire a Harkokin Watsa Labarai tana da fiye da kashi 70 cikin ɗari na mahalarta daga ɓangaren masu zaman kan su, kuma tana daidaita ayyukan ta da mafi kyawun ƙa’idojin duniya domin tabbatar da cewa masana’antu ne ke jagorantar cigaban ƙwarewa.”
Ziyarar ta samu halartar Babban Sakataren Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mista Chinasa Ogbodo; Darakta Janar na NTA, Malam Abdulhameed Dembos; Darakta Janar na FRCN, Dakta Mohammed Bulama; Darakta Janar na VON, Malam Jibrin Baba Ndace; Darakta Janar na Hukumar Tallata Kayayyaki ta Ƙasa (ARCON), Dakta Olalekan Fadolapo; da kuma Manajan Darakta na Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Malam Ali M. Ali.
No comments