Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Uba Sani Ya Buƙaci Al’ummar Jihar Da Su Yi Rijistar Katin Zabe

 Daga SHEHU YAHAYA, Kaduna Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi kira ga waɗanda suka isa yin rijistar katin zabe a jihar, da su shiga rijistar da hu...

 Daga SHEHU YAHAYA, Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi kira ga waɗanda suka isa yin rijistar katin zabe a jihar, da su shiga rijistar da hukumar zabe ke gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

Gwamnatin ta  bayyana wannan mataki a matsayin muhimmin lokaci na ƙarfafa Dimokraɗiyya da gina shugabanci mai ɗaukar kowa da kowa.

A cikin wata sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa hanjun Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ta bayyana  cewa  “Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna ya bayar da umarnin cewa ba wani ɗan ƙasa mai cancanta da ya kamata a bar shi a baya a wannan muhimmin aikin.

"Wannan ba kawai batun shiga cikin rajista ba ne; yana da nasaba da kare haƙƙin Dimokraɗiyya na jama’ar mu da kuma zurfafa shugabanci na gaskiya wanda ke ɗaukar kowa da kowa.”

“Don haka, Ma’aikatar Yaɗa Labarai tana aiki kafaɗa da kafaɗa da Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi, Hukumar Harkokin Addinai, tare da haɗin gwiwar manyan shugabannin gargajiya da na addini, domin tabbatar da cewa wayar da kai da kuma tura saƙon rajista ya isa kowace mazaba, ƙauye, da unguwa a fadin Jihar Kaduna,” in ji Maiyaki.

Kwamishinan ya ƙara da cewa jagorancin Gwamnan na bai wa haɗin kan al’umma muhimmanci a matsayin ginshiƙin shugabanci na Ɗimokraɗiyya.

“Wannan ƙoƙarin wayar da kai yana nuna hangen nesa na Gwamna na gudanar da mulki mai maida hankali kan buƙatun jama’a, inda kowace murya ke da muhimmanci, kuma kowane ɗan ƙasa yana da rawar da zai taka wajen gina makomar Jihar Kaduna.

“Muna kira ga duk masu ruwa da tsaki, shugabannin al’umma, ƙungiyoyin matasa, ƙungiyoyin mata da kuma masu fafutukar ci gaban al’umma da su mara wa wannan yunƙuri baya domin ganin an cimma nasara tare.” In ji shi.
 

No comments