Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zamfara Babban Wuri Ne Na Aikin Noma Mai Amfani Da Hasken Rana, Inji Gwamna Lawal

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa Jihar Zamfara na cin gajiyar tsananin hasken rana a duk shekara, inda ya sanya ta a matsayin wurin da ya ...


Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa Jihar Zamfara na cin gajiyar tsananin hasken rana a duk shekara, inda ya sanya ta a matsayin wurin da ya dace da gonaki masu amfani da hasken rana da na’urorin samar da wutar lantarki masu zaman kansu.

Hukumar Raya Wutar Lantarki ta Karkara (REA) ta gudanar da taron tattaunawa da masana na jihar Zamfara a ranar Larabar da ta gabata a Abuja, inda ta tattaro masu ruwa da tsaki a fannin lantarki a ci gaba da tarukan dabarunta na jiha zuwa jiha.



A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa taron ya mayar da hankali ne kan farfaÉ—o da harkar wutar lantarki ta Zamfara, domin inganta zamantakewar al’umma, da ci gaba, da Æ™irÆ™ire-Æ™irÆ™ire ta hanyar samar da tsayayyen lantarki.

Sanarwar ta Æ™ara da cewa, a yayin taron an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Yankunan Karkara, sannan aka tattauna da masu ruwa da tsaki, tambayoyi da amsoshi, ra’ayoyi, da kuma alÆ™awura.

A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya ce ya gaji matalauciyar gwamnatin a bangaten lantarki.

Ya ci gaba da cewa, “An katse Æ™ananan hukumomi da yawa daga babban lantarkin Æ™asa. An sace wayoyin lantarki da dama, wasu kuma sun lalace, wasu muhimman ababen more rayuwa sun durÆ™ushe a cikin shekaru saboda watsi da su, sannan masana’antu da kasuwancinmu sun gurgunta saboda rashin ingantaccen wutar lantarki.

"Duk da haka, mun zaɓi kada mu shiga wasan zargi, a maimakon haka, mun mayar da martani ga ƙalubalen da muka gamu da su tare da hangen nesa mai muhimmanci, ƙuduri aiwatar da aiki da kuma yanke hukuncin cikin gaggawa.

“Tun daga wannan lokacin ne gwamnatinmu ta fara aikin sake rubuta wannan labari ta hanyar sanya hanyoyin samar da wutar lantarki a cikin dabarun ci gabanmu, mun Æ™addamar da É—aya daga cikin shirye-shiryen samar da taransfoma na Æ™asar nan, inda muka tura taransifoma sama da guda 150 a cikin birane da Æ™auyuka.

“A tare da haÉ—in gwiwar Kamfanin Samar da Wutar Lantarki ta Kaduna mun maido da wutar lantarki a Æ™ananan hukumomi shida, kuma mun sake haxe wasu guda bakwai, waÉ—anda wasu daga cikinsu ba su da wutar lantarki sama da shekaru goma, wannan Æ™oÆ™ari na cikin wani shiri na zaburar da masana’antu, da kuma buÉ—e kasuwanni masu zaman kansu.

Gwamna Lawal ya ce, Zamfara tana ba da damammaki masu kyau don saka hannun jari a bangaren lantarki. "An albarkace mu da hasken rana mai tsananin ƙarfi a duk shekara, wanda ya sa mu zama wuri na farko da gonakin hasken rana za su samu habaka cikin sauri.

“Idan aka duba za a babban damar da madatsar ruwa ta Bakalori ke da shi, kadara ce ta samar da wutar lantarki da ba a yi amfani da ita ba, tare da yanki sama da hekta 30,000 na ban ruwa. Wannan haÉ—in gwiwa na hasken rana yana ba da damar Æ™addamar da hanyoyin samar da lantarki wanda zai iya ci gaba da Æ™arfafa birane da karkara.

“Bangaren nomanmu wani muhimmin batu ne, a kullum jihar Zamfara tana cikin jerin manyan jihohin da ke girbin gero, dawa, waken soya, da gyaÉ—a a Nijeriya, muna sake fasalin wannan fanni ta hanyar ingantattun kayan aiki, injininan noma na zamani, da gyaran ban ruwa.

“Babban misalin sabunta kayan aikin mu shi ne filin jirgin sama na Gusau da filin jirageb É—aukar kaya da ke kusa da shi, wanda aka tsara shi a matsayin Æ™ofa ga fasinjoji, kasuwanci da saka hannun jari.

"Don cimma burinmu na noma, muna nufin wannan ginin ya zama filin jirgin sama na farko a Nujeriya wanda zai samu wutar lantarki aƙalla kashi 50 cikin 100, kuma zai bai wa RESCO damar jagorantar sufurin jiragen sama mai ɗorewa."

Tun da farko, Manajan Daraktan REA, Abba Abubakar Aliyu, ya tabbatar wa Gwamna Lawal ƙudirin hukumar na samar da kayayyakin wutar lantarki a jihar Zamfara.

"A karon farko a tarihin Nijeriya an yi taswirar ƙasar baki ɗaya, kuma hakan ya nuna adadin mutanen da ba su da wutar lantarki da kuma wurin da suke da shi, yanayin al'ummarsu da kuma buƙatar wutar lantarki, hakan ya taimaka wa RESCO da kuɗi, kuma gwamnatin jihar ta samu dabarar da za a bi don ganin cewa waɗannan mutanen sun samu wutar lantarki."


No comments