Biyo bayan farmakin da jami’an tsaro na haɗin gwiwa da Askarawan Zamfara suka kai, ’yan bindigar da ke barna a yankin Arewa maso Yamma sun...
Biyo bayan farmakin da jami’an tsaro na haɗin gwiwa da Askarawan Zamfara suka kai, ’yan bindigar da ke barna a yankin Arewa maso Yamma sun yi amfani da farfaganda don ƙara wa mambobinsu ƙwarin gwiwa. Ɗaya daga cikin irin waɗannan farfaganda shi ne tilasta wa waɗanda suka sace da ƙarfin bindiga amsa cewa su ‘yan uwan manyan jami’an gwamnati ne da kuma roƙon a biya kuɗin fansa domin a sako su.
Idan dai ba a manta ba, a sakamakon zazzafar farmakin da aka kai wa ’yan bindigar, an kashe wani ɗan uwa ga Bello Turji, fitaccen shugaban ‘yan ta'adda tare da sauran ‘yan bindiga da dama a kwanakin baya. A ƙarshen makon da ya gabata ne aka kashe riƙaƙƙen ɗan bindiga Yellow Ɗanbokolo kuma ƙani ga Bello Turji, bayan wani artabu tsakanin ‘yan kungiyar sa da dakarun Askarawan Zamfara a Shinkafi ta Jihar Zamfara.
Ɗanbokolo, wanda ake kyautata zaton ya fi Turji zalunci, an kashe shi tare da wasu yaran sa. Ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu a harin da aka kai masa kuma an binne shi a ranar Asabar.
An samu labarin cewa mazauna yankin sun ce sama da 'yan ta'adda 170 ne suka mutu tare da kwamandan. Kisan Ɗanbokolo, ɗan uwan Turji Bello, tare da wasu yaran sa da dama, an ce ya haifar da babban koma baya ga gungun ‘yan bindigar, wanda hakan ya sa suka fara yaɗa farfagandar ta hanyar tilasta wa waɗanda suka sace yin iƙirarin ƙarya.
Wani faifan bidiyo ya nuna wasu mutane biyu masu matsakaitan shekaru biyu — ɗaya sanye da kaftan mai launin ruwan ƙasa, ɗayan kuma kaftan kore mai haske. A cikin faifan bidiyon, matasan biyu sun bi umarnin ‘yan fashin yayin da suke amsa tambayoyi.
A cikin faifan bidiyo na farko, wanda ya ɗauki tsawon daƙiƙa 26, an ga ‘yan bindigar suna nuna bindiga suna tambayar mutanen, a cikin harshen Hausa, tambayoyi kamar haka:
'Yan bindiga: Daga ina aka sace ku?
Waɗanda aka yi garkuwa da su: Kucheri.
'Yan bindiga: Ina ku ka je?
Waɗanda aka yi garkuwa da su: Mun je Funtuwa ne.
'Yan bindiga: Me ku ka je yi a Funtuwa?
Waɗanda aka yi garkuwa da su: Mun je masana'antar mu ta burodi ne.
Bidiyo na biyu mai tsawon daƙiƙa 30, ya nuna yadda ‘yan bindigar ke yi wa mutumin da ke sanye da kaftan kalar ruwan ƙasa tambayoyi game da dangantakarsa da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal.
'Yan fashi: "Mene ne alaƙar ka da Dauda?"
Wanda aka sace: "Ni ɗan uwansa ne."
’Yan bindigar sun ci gaba da cewa, “Uba da uwa ɗaya ku ka haɗa?”
Wanda aka yi garkuwa da shi ya amsa "eh" cikin izza saboda tsoron kada a harbe shi nan take.
Sai ‘yan bindigar suka yi ihu, “Ka faɗa da babbar murya.” Ya maimaita sau biyu bisa tursasawa cewa shi kanin Dauda Lawal ne.
Sai ‘yan bindigar suka ce, ‘Idan ba mu sami kuɗin fansar da muka bukata ba, za mu kashe ku.
"Ka ce su kira Dauda ya turo kuɗin."
GASKIYAR MAGANA:
Binciken mu ya gano cewa maganar ƙarya ce domin babu ɗaya daga cikin waɗanda aka sace da ke da alaka da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal.
Wani bincike da PREMIUM TIMES ta yi ya nuna cewa gwamnan yana da 'yar uwa ɗaya ce kawai, kuma mace ce, ba namiji ba.
Wanda aka yi garkuwa da shi da aka nuna a cikin faifan bidiyon ya na cikin ruɗani ne, mai yiwuwa saboda matsin lamba daga ‘yan bindigar da suka buƙaci ya bi umarninsu.
Mun tuntubi mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, domin tabbatar da ko ɗaya daga cikin mutanen biyu na da alaƙa da gwamnan. Ya ce, babu ko ɗaya daga cikin su da ke da wata alaƙa da gwamnan, ya ƙara da cewa lamarin wani sabon shiri ne na ‘yan bindiga na ganin sun ɗauki hankulan jama’a tare da ƙara wa mambobinsu kwarin gwiwa.
Mai magana da yawun gwamnan ya ce, “Idan aka kalli wannan faifan bidiyo cikin tsanaki, za a iya ganin yadda waɗanda aka sace suka shiga cikin ruɗani, na yi imanin cewa wannan wani sabon salo ne da ‘yan bindigar suka ɗauka, amma, babu ɗaya daga cikin waɗanda aka sace da ke da alaƙa da gwamna.
"A halin yanzu gwamnati na ɗaukar matakai don tabbatar da ceto wadanda lamarin ya shafa da kuma haɗa su da iyalansu."
No comments