Bayan shafe tsawon shekaru bakwai ana shari’a, babbar kotun jihar Kano ta yanke wa Aminu Muhammad hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin...
Bayan shafe tsawon shekaru bakwai ana shari’a, babbar kotun jihar Kano ta yanke wa Aminu Muhammad hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe wata yarinya ‘yar shekara uku mai suna Rafi’atu Junaidu.
Mai shari’a Maryam Sabo ta yanke hukuncin ne a ranar Larabar da ta gabata, inda ta samu Muhammad da laifin kai yarinya gona a ƙauyen Jibga da ke ƙaramar hukumar Bebeji a shekarar 2018, inda ya shaƙe ta tare da yanke mata jiki.
Bayanai na kotun sun nuna cewa Muhammad ya tsaga cikin yarinyar da fasasshiyar kwalba sannan ya cire mata hanjin ciki, wanda ya kasance wani mummunan tashin hankali.
Shaidu uku da masu gabatar da ƙara da kuma shaidun da lauya mai shigar da ƙara, Barista Badawiyya Shehu Bala ya gabatar, ya kai ga yanke hukuncin.
A yayin shari’ar, an kuma bayyana cewa, mai yiwuwa wani ne wanda ba a san ko wane ne ba ya yi masa alƙawarin N400,000 don aikata kisan.
Har yanzu dai ba a tabbatar da gaskiyar iqirarin wanda ake zargin ba, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan iƙirarin.
Da take bayyana laifin a matsayin "rashin tausayi da rashin imani," Mai shari'a Sabo ta ce ya kamata hukuncin kotun ya zama izina ga wasu.
"Kotu ta sami wanda ake tuhuma da laifi kamar yadda ake tuhuma kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya," inji ta.
No comments