Mataimakin Shugaban kasa Sanata Kashim Shatima ya bayyana cewa Gwamnatin taraya ta kaddamar shirin kawo karshen cin zarafin kananan yara a ...
Mataimakin Shugaban kasa Sanata Kashim Shatima ya bayyana cewa Gwamnatin taraya ta kaddamar shirin kawo karshen cin zarafin kananan yara a Najeriya, tare da tsaurara dokokin kare hakkin yara domin tabbatar da tsaro, mutunci da kuma makomar yan Najeriya.
Shatima ya faɗi hakan ne a yayin da ya ke wakiltar Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a wajen babban taron hadakar kasashen Afrika karo na farko da nufin kawo karshen cin zarafin ƙananan yara wanda ya gudana a babban dakin taro na fadar Shugaban Kasa dake Abuja.
Shettima ya bayyana aniyar gwamnatin tarayya na kafa wata hukumar kare hakkin yara da cigaban su, kana an kaddamar da asusun tallafa wa kananan yara na bai daya, domin rage talauci a gidajen marasa galihu.
Mataimakin ya kara da cewa Shugaba Tinubu ya sha alwashin ganin cibiyoyin Gwamnati masu ruwa da tsaki, ciki har da ma’aikatar mata ta tarayya, za su yi aiki tare wajen bayar da horo da kayan aiki da ake bukata domin jagorantar kare lafiyar yaran Najeriya a dukkanin matakan Gwamnati, ganin cewa aiki ne da ke bukatar zage damtse.
Tun da farko wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya kan cin zarafin yara Dokta Najat Maalla M’jid, ta bukaci shugabannin Afirka da su yi hobbasa wajan aiwatar da ayyuka masu muhimmanci domin kare yara daga cin zarafi
No comments