Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DA ƊUMI-ƊUMI: Iran Da Nijar Sun Ƙulla Yarjejeniyar Yaƙi Da Ta'addanci

Shugaban Rundunar Tsaron Ƙasar Iran, Janar Ahmad Rezaei ya jagoranci wata tawaga zuwa Nijar, inda suka gana da Ministan cikin gida na Nijar....

Shugaban Rundunar Tsaron Ƙasar Iran, Janar Ahmad Rezaei ya jagoranci wata tawaga zuwa Nijar, inda suka gana da Ministan cikin gida na Nijar.

A yayin ganawar, ɓangarorin biyu sun amince da kafa kwamitin ƙwararru domin tattaunawa akai-a kai game da batutuwan da suka shafi tsaro tsaro.

Haka kuma Ministocin sun sanya hannu kan yarjejeniyar da ta haɗa da yaƙi da ta’addanci, hana laifukan ƙetare iyaka gami da yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.

Masana al'amuran yau da kullum suna da hasashen cewa tunda gwamnatin soji ta Nijar ta yanke hulɗa da Turawan Yamma, ciki kuwa har da Farance wacce ita ce ta reneta, to babu makawa za ta nemi taimakon ƙasashe masu cin gashin kansu, masu ci gaba a duniya, kamar dai ita Iran ɗin.

Masanan suna ganin cewa wannan mataki zai taimaka wa ƙasar ta Nijar matuƙa, musamman tun da yanzu babu wata ƙasa da za ta gindaya mata wasu sharuɗɗa. Sannan kuma ga ota Iran ɗin tana burin taimaka wa ƙasashen Afrika.
 

No comments