Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Amince da Kafa Rundunar Masu Tsaron Daji Domin Ƙarfafa Tsaro a Nijeriya

A wani mataki na tabbatar da tsaro da inganta Zaman Lafiya a Najeriya, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da kafa rundunar Masu T...

A wani mataki na tabbatar da tsaro da inganta Zaman Lafiya a Najeriya, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da kafa rundunar Masu Tsaron Daji (Forest Guards) domin tabbatar da tsaron dazuka guda 1,129 da ke faɗin Najeriya.

Shugaban ƙasar ya bayar da umarni kai tsaye cewa sababbin jami’an za su samu cikakken horo da makamai masu inganci domin gudanar da ayyukansu cikin kwarewa da ƙwazo. Babban aikin wannan sabuwar runduna shi ne kora ‘yan ta’adda da miyagu da suke fakewa a cikin dazuka suna aikata muggan laifuka kamar garkuwa da mutane da fashi da makami.

Wannan mataki ya samo asali ne daga haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya da Jihohi, wanda ya nuna cewa ana ɗaukar tsaro a matsayin aikin kowa da kowa. Ofishin mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) da Ma’aikatar Muhalli su ne aka dorawa alhakin aiwatar da wannan sabuwar doka tare da tabbatar da cikakkiyar nasararta.

Wannan tsari zai buɗe dama ga dubban matasan Najeriya su samu aikin yi, tare da bayar da gudunmawa wajen ceton ƙasar daga barazanar ‘yan ta’adda da miyagu. Shugaba Tinubu ya bayyana a fili cewa gwamnatinsa ba za ta bar yanki ko guda ba na ƙasar nan ya faɗa hannun ‘yan ta’adda. Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da za a kwato dazuka da ‘yan ta’adda suka mamaye, a maida su wuraren da za su amfanar da al’umma ta fuskar noma, muhalli, da tattalin arziki.

Wannan tsari ya nuna irin tsayayyen shugabanci da ƙuduri na Shugaba Tinubu wajen ganin Najeriya ta zama ƙasa mai tsaro, mai cigaba, kuma mai ɗorewar zaman lafiya. Ana sa ran wannan runduna za ta taka muhimmiyar rawa wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro da suka dabaibaye ƙasar nan tsawon shekaru.

No comments