Gwamnatin Tarayya ta bayyana ƙudirin ta na yin aiki tare da Majalisar Dokoki da kafafen yaɗa labarai da sauran muhimman masu ruwa da tsaki w...
Gwamnatin Tarayya ta bayyana ƙudirin ta na yin aiki tare da Majalisar Dokoki da kafafen yaɗa labarai da sauran muhimman masu ruwa da tsaki wajen sake duba Dokar Laifuffukan Intanet domin samar da doka da kowa zai yarda da ita kuma za ta yi tasiri.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja bayan ganawar sa da Jakaden Amurka a Nijeriya, Mista Richard Mills.
Ya ce: “Dangane da batun sake duba Dokar Laifuffukan Intanet, za mu bayar da gudunmawar mu ta hanyar aiki tare da Majalisar Dokoki da sauran masu ruwa da tsaki da kafafen yaɗa labarai da kowa baki ɗaya domin tabbatar da cewa mun samu wata doka da kowa zai amince da ita kuma za ta cika manufar ta.”
Idris ya jaddada cewa Gwamnatin Tinubu tana da ƙudirin kare ’yancin faɗin albarkacin baki da ’yancin kafafen yaɗa labarai, waɗanda ya ce su ne ginshiƙan dimokiraɗiyya a ƙasar nan.
Ya ce: “Na bayyana ra’ayi na ga Jakaden, kuma na kuma jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da kare ’yancin faɗin albarkacin baki da kuma rashin takura wa 'yan jarida wajen gudanar da aikin su. Za mu ci gaba da kare wannan.
"Muna ganin aikin jarida da kafafen yaɗa labarai wani muhimmin ɓangare ne na dimokiraɗiyya.
“Babu wata dimokiraɗiyya da za ta yi nasara ba tare da kafafen yaɗa labarai ba."
Sai dai kuma ministan ya buƙaci 'yan jarida da su riƙa amfani da 'yancin da suka samu cikin ƙwarewa da nuna kishin ƙasa.
Ya ce: “Muna kuma amfani da wannan dama wajen ƙarfafa gwiwar 'yan jarida a Nijeriya cewa yayin da suke amfani da ’yancin kafafen yaɗa labarai, su tabbata suna ɗaukar nauyin aikin da muhimmanci.
"Su ci gaba da kasancewa masu sanin hakki, kuma a gaskiya sun kasance, amma muna buƙatar su ƙara jajircewa wajen yaɗa sahihan labarai da nuna kishin ƙasa, domin hakan ne kaɗai zai tabbatar da ɗorewar dimokiraɗiyyar."
Ministan ya tabbatar da ci gaba da inganta wayar da kan jama’a kan kafafen yaɗa labarai da bayanai domin daƙile yaɗuwar labaran ƙarya.
A nasa ɓangaren, Jakaden Amurka, Mista Mills, ya ce ganawar sa da ministan ta kasance mai amfani matuƙa, musamman dangane da ’yancin kafafen yaɗa labarai da kuma sake duba Dokar Laifukan Intanet.
Ya ce: “Na yi wata muhimmiyar ganawa da Minista dangane da ’yancin kafafen yaɗa labarai a Nijeriya da kuma ƙudirin sa na kare wannan dama da ke bai wa mutane damar faɗin albarkacin bakin su.
"Na yaba da jawabin da ya fitar a ranar 3 ga Mayu, wato ranar ’Yancin Kafafen Yaɗa Labarai ta Duniya, inda ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na kare wannan ’yanci.
“Mun kuma tattauna batun sake fasalin Dokar Laifukan Intanet da kuma yadda na buƙaci cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta taka muhimmiyar rawa a cikin wannan sauyi a Majalisar Dokoki.”
Wannan shi ne karo na biyu da Jakaden Amurkan ya gana da Ministan kan batutuwan da suka shafi ’yancin kafafen yaɗa labarai a Nijeriya.
No comments