Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Abubuwan Da Aka Cimmawa A Taron Gwamnonin Arewa

Gwamnoni da kuma Sarakunan gargajiya na Arewacin Nijeriya sun gudanar da taro a Kaduna, domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaro da suka...


Gwamnoni da kuma Sarakunan gargajiya na Arewacin Nijeriya sun gudanar da taro a Kaduna, domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi yankin.

Taron ya gudana ne a gidan gwamnatin jihar ta Kaduna, inda suka tattauna kan matsalar talauci da yaran da ba su zuwa makaranta da kuma sauran al’amura da suke damun yankin.

Gwamnonin jihohin Katsina da Zamfara da Kebbi da Gombe da Neja da Filato da Yobe da Jigawa da Kogi da Adamawa da kuma Zamfara na cikin waÉ—anda suka halarci taron.

A É“angaren sarakunan gargajiya kuma akwai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III da Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli da Etsu na Nupe da Sarkin Zamfara da Sarkin Bauchi da Sarkin Ilorin da Sarkin Keffi da sauransu.
Sarakunan gargajiya da gwamnonin Arewa da suka halarci taron

Gwamnonin sun yaba wa ƙoƙarin Shugaban Nijeriya Bola Tinubu na magance matsalar tsaro a faɗin ƙasar, sai dai sun buƙaci tana a ƙara ƙaimi domin a cewarsu an fara mayar da hannun agogo baya.

Gwamnonin sun ce yadda Boko Haram ke ƙoƙarin dawo da ayyukanta a wasu sassan Arewa maso Gabas, da kashe-kashe a Arewa ta Tsakiya ne ya sa suke kira da a yi garambawul a ɓangaren tsaro.

Da wannan ne Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta yi kira da a Æ™ara samun haÉ—in kai tsakanin jami’an tsaron gwamnatin tarayya da na jihohi da Æ´an sa-kai.

Shugaban ƙungiyar, Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan a sanarwar bayan taron da aka yi ranar Asabar a Kaduna.

“Ƙungiyar za ta haÉ—a Æ™arfi da Æ™arfe da Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya domin samar da hanyoyin taimakon jami’an tsaron gwamnatin tarayya wajen magance matsalar da Æ™asar ke fuskanta,” inji shi.

Sannan ya ce ƙungiyar za ta kafa kwamitin haɗin gwiwa domin samar da tsarin bai-ɗaya na tsaro domin sa ido kan tsaron iyakokin jihohi.

Haka kuma Æ™ungiyar ta sake nanata goyon bayan da kafa ’yan sandan jiha, inda gwamnonin suka yi kira ga majalisar Æ™asar da ta gaggauta É—aukar matakin yin doka domin tabbatar da Æ™irÆ™irar ’yan sandan na jiha.

Ga wasu abubuwa biyar da Gwamnonin Arewa suka tattauna a taron:

1. Ƙungiyar ta yaba wa shugaba Bola Tinubu kan kokarin da yake a fannin samar da tsaro a Arewa.

2. ⁠Ƙungiyar za ta haÉ—a kai da kungiyar Gwamnonin Nijeriya domin karfafa fannin tsaro a yankin.

3. ⁠Ƙungiyar za ta É“ullo da tsarin inganta tsaro a yankin tun daga tushe.

4. ⁠Ƙungiyar ta buÆ™aci a yi gaggawar É—aukar matakan samar da tsaro a iyakokin jihohin yankin.

5. ⁠Ƙungiyar ta jaddada goyon bayanta kan samar da ‘yan sandan jihohi, inda ta buÆ™aci Majalisar Tarayya ta tabbatar da hakan.

Ƙungiyar ta ce, za su sake zama a ranar 30 ga watan Agustan 2025.

No comments