A yayin da ake tsaka da jin kiraye-kirayen jam'iyyun adawa na neman Tsohon Shugaban Nijeriya Goodluck Ebele Jonathan ya fito takara a za...

Jaridar The Punch ta ta ruwaito Mrs Jonathan ta bayyana hakan ne a daren Asabar a birnin Abuja, inda ta karɓi lambar yabo ta 'Jagorar matan shekara ta 2025' daga kamfanin Accolade Dynamics Limited.
Uwargidan tsohon shugaban ƙasar ta ƙara da cewa maimakon komawa fadar Mulki ta Villa, ta kudiri aniyar mara wa Shugaba Tinubu baya a zaben shekarar 2027, duba da alaƙar ƙut da ƙut da ke tsakaninsu da uwargidan girma shugaban ƙasar, Sanata Oluremi Tinubu da kuma kyawawan aiyukan da Shugaban ya faro.
Madam Patience ta Kore rade-radin da ake yadawa kan aniyarsu ta yin takarar Shugaban kasar inda ta ce
"Ina tare da ƙawata Remi, Kawata babbar mace ce. Na ce mata zan yi kamfen da ita. Ba na ɓoye-ɓoye. Ba zan yi takara ba. Ba zan koma Villa ba. Ko kun kira ni, ba zan je ba."
No comments