Gwamnatin tarayya ta buƙaci Bankin Musulunci ya ƙara zuba jari a harkar kasuwancin abinci na Halal a duk faɗin ƙasar nan. Mataimakin shugaba...
Gwamnatin tarayya ta buƙaci Bankin Musulunci ya ƙara zuba jari a harkar kasuwancin abinci na Halal a duk faɗin ƙasar nan.
Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ne ya bayyana buƙatar a yayin da ya yi wata ganawa da tawagar bankin a fadar Shugaban Kasa.
Mataimakin shugaban ya yi nuni da yadda Nijeriya ta samu bunƙasa a harkokin kasuwanci a ƙarƙashin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi na magance ƙalubalen da ake fuskanta a muhimman ɓangarorin tattalin arziki da suka haɗa da zuba jari akan 'yan ƙasa da samar da abinci mai gina jiki, da bunƙasa noma, da kiwon lafiya, da ilimi, da kasuwanci na zamani.
Ya kuma ƙarfafa wa bankin gwiwar kan yin amfani da yanayin da ake ciki a matsayin lokaci mafi dacewa na zuba jari a Najeriya, yana mai nuni da sauye-sauye a sassa masu mahimmanci da gwamnatin ta samar
Baya da bunƙasa tattalin arzikin Halal, Kashim Shettima ya buƙaci bankin da ya inganta kasuwanci a bangaren fasahar zamani, da hada-hadar kudi da sabon shirin Agro-Processing Zones (SAPZ) na samar da muhalli na musamman ga noma da ilmi da ababen more rayuwa da kiwon lafiya.
Ita ma Tawagar bankin Musulunci, karkashin jagorancin Mista Hammad Hundal, ta nuna gamsuwarta da tsare-tsaren gwamnatin shugaba Tinubu inda ta bayyana kudurinta na fifita ƙudurorin Shugaban a matsayin hanyar haɓaka farfado da walwala da magance talauci, da kuma haifar da ci gaban tattalin arziƙin.
No comments