Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al'ummar jihar Kano da ma ƙasar nan gaba ɗaya shi ne matak...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al'ummar jihar Kano da ma ƙasar nan gaba ɗaya shi ne mataki na nasara da jin daɗi a kowane yanayi.
Hon. Murtala Husaini S/Gida, Ciroman Sarkin noman Gaya, Wakilin Gonar Galadiman Kano, Kasilan Mazabar Balam ne ya bayyana hakan da yake zantawa da 'yan jarida a taron naɗin sabbin sarautu da aka yi a fadar Kano.
Ya ce suna mutuƙar farin ciki da naɗin da aka yi na ɗaga likkafar Turakin Kano Munir Sanusi ya zama Galadiman Kano, suna fata Allah ya taya shi riƙo. Daga nan ya gode wa Sarkin Kano Muhammad Sanusi kan ƙoƙarin sa na haɗa kan masarautar.
Ya ce wannan taro na naɗin Galadima da sauran sarautu da mai martaba Muhammad Sanusi ya yi, ya daɗa fito da kima da ƙoƙarin masarautar Kano na haɗa kan al'umma da inganta zaman lafiya da cigaba.
A ƙarshe Hon Murtala Hussaini S/gida ya yi kira ga al'ummar jihar Kano su ci gaba da bai wa Gwamnatin jihar Kano da masarautar Kano haɗin kai da goyon baya domin cimma nasara a ƙoƙarin da suke na kare martabar al'umma da ci gaban jihar.
No comments