Daga Ibrahim Muhammad, Kano Kungiyar Kwadago ta kasa reshen jihar Kano ta bayyana cewa zata cigaba da goyon bayan Gwamnan jihar Kano Inji...
Kungiyar Kwadago ta kasa reshen jihar Kano ta bayyana cewa zata cigaba da goyon bayan Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf akan irin ayyuka da yake na kyautatawa kyawawan manufofiin da yake aiwatarwa ma'aikata da al'ummar Kano baki daya.
Shugaban Kungiyar reshen jihar Kano Kwamared Kabiru Inuwa ne ya bayyana goyon bayan ma’aikatan ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a yayin bikin ranar ma’aikata ta duniya na 2025.
An dai gudanar da bikin ranar ma’aikata ta Duniya ne a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar mata a ranar Alhamis, 1 ga Mayu, 2025.
Kwamared Kabiru Inuwa ya yi nuni da cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa tarihi a matsayin shi ne Gwamna na farko a faɗin ƙasar nan da ya soma aiwatar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na N71,000
Ya bayyana hakan da cewa jaruntace da Gwamnan ya cancanci a yaba masa, domin ya taimaka wajen rage wa ma’aikata raɗaɗin halin ƙuncin rayuwa da matsin tattalin arzikin da suke ciki.
Shugaban ƙungiyar na jihar Kano Kwamared Kabiru Inuwa ya ƙara da cewa, sannan Gwamnan ya zo ya yi ƙarin mafi ƙarancin fansho daga N5,000 zuwa N20, 000 da kuma biyan kuɗaɗen garatuti da ake bi bashi a Gwamnatocin baya, wannan mataki ne da ke nuna kulawar Gwamnan ga tsofaffin ma’aikata
Shugaban ya tabo ayyuka da dama da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke aiwatarwa domin bunƙasa ci gaban al'ummar jihar Kano da kuma ma'aikata a ɓangarorin ilimi da lafiya da sauran fannonin.
Daga nan Kwamared Kabiru Inuwa ya ce ma'aikatan jihar Kano a shirye suke su ci gaba da bai wa Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf haɗin kai da goyon baya akan kyawawan manufofinsa na ciyar da jihar gaba
No comments