Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Yi Kira Da A Kiyaye Mutuncin Mata

Daga Hussaini Yero, Gusau Uwargidan Gwamnan jihar Zamfara Hajiya Huriyya Dauda ta bayyana takaicin ta kan yadda ake samun Jami'an tsaro ...

Daga Hussaini Yero, Gusau

Uwargidan Gwamnan jihar Zamfara Hajiya Huriyya Dauda ta bayyana takaicin ta kan yadda ake samun Jami'an tsaro da laifin cin zarafin Mata, don haka ta yi kira ga mahukunta da su sanya duk Jami'an tsaro da aka kama da cin zarafin Mata a kafafen yadlÉ—a Labarai, kamar yadda su ma su ke gabatar da masu laifi ga 'Yan gidan Talabijin da Rediyo da Jaridu don ya zamo izina ga sauran Jami'an tsaro.

Hajiya Huriyya Dauda ta bayyana haka ne a Larabar da ta gabata, rana ta uku na yaƙi da cin zarafin Mata, wanda aka yi ma fyaɗe, da marasa galihu da ake tauye ma haƙƙoƙin su a Gusau babban birnin jihar.

A jawabin ta, Huriyya Dauda ta bayyana cewa a jawaban da aka gudanar a yanzu ya tabbatar da cewa, fitattun mutane ne, kuma sanannu ake kamawa da laifin cin zarafin Mata. "Don haka muka Æ™addamar da kwamitoci a Ƙananan Hukumomi don yaÆ™i da masu aikata wannan mumunan laifi don kawo Æ™arshen su," in ji ta. 

Ta ƙara da cewa, "Kuma yau ga Littattafai nan na Turanci mun fasara su zuwa Hausa za mu raba don mutane su gane illar cin zarafin Mata da kuma hukuncin da mai yi zai gamu da shi."

Hajiya Huriyya ta ƙara da cewa, ba fyaɗe ba ne kaɗai cin zarafin Mata, akwai rashin ba su haƙƙin su na kulawa daga mazajan su na rashin abinci da karatun 'ya'ya mata da sauran su.

Dan haka doka za ta yi aiki akan duk wanda aka kama a Zamfara da waÉ—annan munanan laifuka.

 

No comments