Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana cewa sakamakon iya shugabanci da jagorancin siyasa irin na tsohon Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdul...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana cewa sakamakon iya shugabanci da jagorancin siyasa irin na tsohon Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, yanzu jam'iyyar APC sai ƙara tagomashi take yi a jihar Kano dama ƙasa baki ɗaya.
Hon. Kamalu Baƙo Lamido ne ya bayyana hakan da yake zantawa da 'yan jarida a yayin ɗaurin auren ɗaya daga cikin Dattawan jam'iyyar APC, Alhaji Nasiru Aliko da aka yi a Unguwar Koƙi ta cikin Kano.
Ya ce tun da Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya zama shugaban jam'iyyar APC na ƙasa sai daɗa karɓuwa take yi. Domin ko a zaɓukan da aka yi na Gwamnoni a wasu jihoh, ai APC ce ke yin nasara, har ma inda jam'iyyar 'yan hamayya suke da Gwamna su suka yi nasara.
Alhaji Kamalu Bako Lamido ya ce wannan ya nuna cewa ƙwarewa da gogewa ta jagoran siyasar su, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a siyasa, dama ya taɓa faɗa cewa, shi siyasa ya karanci siyasa ne, ba a kan hanya ya tsince ta ba, wannan irin nasarori da ake samu ya daɗa tabbatar musu da sanin sa na siyasa.
Haka kuma, Hon. Kamalu ya bayyana fitaccen ɗan siyasar nan, ɗaya daga cikin Dattawan a jam'iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Nasiru Aliko Koƙi da cewa mutum ne mai son zaman lafiya da kyakkyawar mu'amala tsakaninsa da al'umma, ba kawai 'yan siyasa ba , da ma kowane irin Mutum, shi ya sa duk wata hidima da ta taso masa ɗibin mutane ke halarta.

No comments