Daga Musa Muhammad Cikin wani ɗan ƙaramin garambawul da ya gudanar a gwamnatinsa, Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya sauke mai kula da...
Cikin wani ɗan ƙaramin garambawul da ya gudanar a gwamnatinsa, Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya sauke mai kula da ma'aikatar harkokin cikin gida da tsaro, Mista Samuel Aruwan, inda nan take ya naɗa Dr. James Atung Kanyip a matsayin Kwamishinan ma'aikatar.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Ibrahim Musa ya bayyana cewa, Gwamnan ya kuma naɗa wata gogaggiyar 'yar jarida, Hajiya Farida Abubakar Ahmad a matsayin shugabar Hukumar kafafen yaɗa labaran jihar ta KSMC.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Gwamna Uba Sani ya naɗa Ibrahim Tanko Mohammed a matsayin Kwamishinan kuɗi, Barde Yunana Markus a matsayin Kwamishinan ma'aikatar jin ƙai.
Ibrahim Musa ya kuma bayyana cewa Gwamna Uba Sani ya naɗa mashawartansa na musamman, waɗanda suka haɗa da Vitus Azuka Ewuzie na harkar Shari'a, Francis Damina na harkar bincike da tattara bayanai, Hon. Victor Mathew Bobai na harkar jama'a, Abdulmutallib Isah na ayyuka na musamman da Abdulhaleem Ishaq Ringim na harkar tattalin arziki.
.jpeg)
No comments