Daga Ibrahim Muhammad, Kano Kamfanin Ɗangote ya samu gagarumin yabo bisa ɗaukar nauyin bikin baje kolin kasuwanci na Kano karo na 45, wanda...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Kamfanin Ɗangote ya samu gagarumin yabo bisa ɗaukar nauyin bikin baje kolin kasuwanci na Kano karo na 45, wanda aka buɗe a ƙarshen makon da ya gabata, misamman a gudumawarsa wajen ci gaban arzikin ƙasa.
Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar da shugaban cibiyar masana’antu, ma’adinai da noma na Kano (KACCIMA) Alhaji Garba Imam suka yi wannan yabo a lokacin da suka ziyarci rumfar kamfanin a wurin baje kolin.
Ministan ya shaida wa mahalarta taron cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta amince da rawar da kamfanonin Ɗangote ke takawa.
Minista Badaru ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatin tarayya na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali, sannan ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da mara wa gwamnati baya da addu’o’i tare da ci gaba da aminta da jami’an tsaro, wanda jajircewarsu na da matuƙar muhimmanci wajen ganin an samu ci gaba.
Shi kuwa Shugaban cibiyar, Alhaji Garba Imam ya yaba wa kamfabin Ɗangoten ne bisa goyon baya da haɗin gwiwar da suke yi, inda ya ƙara da cewa kamfanin ya dage wajen ɗaukar nauyin gudanar da taron baje kolin na shekara-shekara.
Da yake zantawa da manema labarai, Darakta Janar na KACCIMA Alhaji Sabiu Umar Yola ya ce, “Dangantakar KACCIMA da Ɗangote ta kasance mai muhimmanci sosai.
Ya ce taken wannan shekara na da nufin ƙarfafa gwiwar ‘yan Nijeriya wajen samo wasu kayan da za a fitar a ƙasashen ƙetare maimakon ɗanyen mai.
A cikin wata sanarwa da fito daga sashen Sadarwa na Kamfanin Ɗangote, ta ce bikin baje kolin da cibiyar kasuwanci da masana’antu, ma’adinai da noma ta Kano ta shirya, ya yi daidai da hangen nesa na rukunin Ɗangote na bunƙasa tattalin arziki.

No comments