Daga Musa Muhammad, Kaduna Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya kasafta kashe kuɗi Naira Biliyan 790 a kasafin kuɗin shekara mai zuwa ta ...
Daga Musa Muhammad, Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya kasafta kashe kuɗi Naira Biliyan 790 a kasafin kuɗin shekara mai zuwa ta 2025, wanda ya fi mayar da hankali ga muhimman fannonin da suka shafi abubuwan more rayuwa, kyautata rayuwar jama'a, tsaro da harkar noma.
A yayin da ya ke miƙa kundin kasafin kuɗin ga zaure majaliasar Dokokin jihar a Litinin ɗin nan, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta tsara ɗaukar tsauraran matakai wajen tafiyar da hanyoyin kuɗaɗen da ake samu.
Gwamna Uba Sani ya ce, an ware Naira Biliyan 553 a kasafin na 2025 don gudanar da manyan ayyuka, sannan Naira Biliyan 237 don ayyukan yau da kullum.
Ya ce, kaso na manyan ayyuka zai mayar da hankali ga ayyukan inganta rayuwar jama'a, waɗanda suka shafi gina hanyoyin karkara, kayan kula da lafiya a ƙananan ɗakunan shan magani, harkar ilimi da gina gidaje.
Gwamnan ya ce a waɗannan kuɗaɗe da aka kasafta, an ware Naira Biliyan 206.6 ga harkar ilimi, wanda shi ya kwashe kashi 26.14 cikin 100 na kasafin.
Sanata Uba Sani ya ƙara da cewa, ‘’A waɗannan kuɗaɗe na ilimi, za a gina sabbin makarantu, gyara waɗanda ake da su, ɗaukar sabbin Malamai, horar da Malaman da ake da su, tare da samar da wadatattun kayan koyarwa."
Kasafin kuɗin, kamar yadda Gwamnan ya gabatar, ya yi bayani filla-filla yadda za a kashe kuɗaɗen a dukkan fannonin da aka tsara.
.jpeg)
No comments