Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaban Karamar Hukumar Dala, Mutum Ne Jajirtacce -Ummi Ƙofar Ruwa

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Mai baiwa shugaban Ƙaramar Hukumar Dala shawara akan muhalli, Hajiya Ummi Alasan Ƙofar Ruwa ta  bayyana godiya g...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Mai baiwa shugaban Ƙaramar Hukumar Dala shawara akan muhalli, Hajiya Ummi Alasan Ƙofar Ruwa ta  bayyana godiya ga Gwamnan jihar Kano da shugaban ma'aikatan Gidan Gwamnat, Shehu Sagagi da 'yan majalisar Dala da  Kwamishina Ibrahim Namadi da jagoran Kwankwasiyya na Dala, Dayyabu Ahmad  Maiturare bisa goyon bayansu wajen bata muƙamin.

Ta ce, sun sami shugaban Ƙaramar Hukumar Dala Hon. Suraj Imam Mutum ne jajirtacce mai ilimi na zamani da na addini, wanda yake yin ƙoƙarin haɗin kai a wannan tafiya da suke ta Kwankwasiyya amana.

Hajiya Ummi Alasan Ƙofar Ruwa ta kuma yi nuni da cewa matsayin da aka ba ta, na mai bayar da shawara akan muhall, an sanya ƙwarya a gurbin ta, domin ita dama ba ta son ta ga ƙazanta ko yaya take, ko a Unguwar su ta kan fito da yara a yi aikin gayya na kwata a gyara a kwashe.

Don haka ta ce za su bada shawara ga shugaban Ƙaramar Hukumar Dala, Hon. Suraj Imam domin ganin an samu nasarar kyautata tsarin muhalli da bin doka, wanda hakan zai taimaka wajen  tabbatar da ƙa'ida.

Ta ƙara da cewa yanzu wannan muƙami ya ƙara mata ƙwarin gwiwa da za ta bada shawara akan inda ta ga ya kamata a gyarada inda ta ga ba daidai ba, a yi daidai. Donn haka ta ji daɗi da wannan dama da aka ba ta.

A ƙarshe Hajiya Ummi Alasan ta yi kira ga al'ummar Dala akan su ba ta haɗin kai da goyon baya, sannan kuma ƙofarta za ta zama a buɗe, a zo a ba ta shawara, idan an ga ta yi kuskure a sanar da ita domin ta gyara.

No comments