Daga Ibrahim Muhammad, Kano Gwamnatin Jihar Kano ta zargi mai shari’a Simon Amobeda na Babbar Kotun Tarayya a jihar da nuna son zuciya a sha...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta zargi mai shari’a Simon Amobeda na Babbar Kotun Tarayya a jihar da nuna son zuciya a shari’ar zaɓen Ƙananan Hukumomi da aka gabatar a gabansa.
jam’iyyar APC ce dai tare da wasu masu ruwa da tsaki suka shigar da ƙara suna neman kotun ta bayyana cewa ba a samu zaɓaɓɓun shugabannin Ƙananan Hukumomi ba a jihar Kano.
A yayin zaman fara sauraren ƙorafe-ƙorafen da aka shigar ranar Juma’a, Antoni Janar na Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Isa Haruna Dederi, ya nemi Mai Shari’a Amobeda ya janye kansa daga shari’ar saboda zargin nuna son zuciya da ya ce Alƙalin ya yi a lokuta da dama a kan gwamnatin Kano.
A cikin takardar da ya gabatar, Dederi ya yi zargin cewa mai shari’ar yana da wata ƙiyaiya a zuciyarsa da ya nuna ga gwamnatin jihar da hukumominta tun bayan da aka shigar da wani ƙorafi ga Hukumar Kula da Alƙalai ta ƙasa (NJC) da ke zarginsa da cin gajiyar iko da kuma bayar da umarni ba bisa ƙa’ida ba.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta lura da waɗansu abubuwan da ba su dace ba, musamman game da shari’o’in da suka shafi mutanen da ke da alaƙa da siyasa, musamman waɗanda ke cikin jam’iyyun adawa, da aka gabatar gabansa. Wannan, a cewar gwamnatin, yana nuna wata alaƙa tsakanin mai shari’ar da wata jam’iyyar adawa.
Gwamnati ta kuma ce “Mai shari’ar ya sha fitowa a jaridu yana barazanar fallasa wani jami’in gwamnatin Jihar Kano da ya rubuta ƙarar a kansa, yana nuna fushinsa tare da ƙoƙarin tabbatar da cewa ƙarar ba ta dace ba.”
Sai dai mai Shari'a Amobeda, ya nuna rashin amincewa da buƙatar da gwamnatin ta gabatar na ya janye kansa daga shari’ar, ya ce ba ya goyon bayan wani ɓangare kamar yadda ake zarginsa, sai dai yana goyon bayan adalci ne kawai.

No comments