Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

KWAMISHINAN DA AKA ZARGA DA LALATA: Mijin Matar Yi Fatali Da Hukuncin Kotu

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Rahotanni na nuni da cewa, Malam Nasiru Buba, mijin matar nan da ake zargin Kwamishinan ayyuka na musamman na ji...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Rahotanni na nuni da cewa, Malam Nasiru Buba, mijin matar nan da ake zargin Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara ya yi lalata da ita, ya ƙi amincewa da hukuncin da wata kotu ta yanke na wanke Kwamishinan daga zargin.

Ina dai ba a manta ba, wata babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Kano ta yi watsi da Æ™arar da ake yi wa Sankara a ranar Litinin É—in da ta gabata, saboda rashin samun hujjoji.

Alƙalin kotun, Ibrahim Sarki Yola ya yi fatali da ƙarar bayan da ya amince da rahoton 'yan sandan da ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa, Sankara ya aikata zargin da ake yi masa.

To, amma mijinatar, Malam Buba ya bayyana wannan hulunci a matsayin rashin adalci, inda ya dage cewa ya bayar da ƙwararan hujjojin da za su tabbatar da iƙirarin nasa.

Ya ce, “Na gabatar da É—aruruwan shaidun da za a iya tantancewa, waÉ—anda suka haÉ—a da hotuna 854, bidiyoyi fiye da 100, bayanan murya fiye da 200 a manhajar WhatsApp, da bayanan kiran waya na sama da sa’o’i 500. Idan kotu ta jefar da waÉ—annan hujjoji, Allah da kuma mutanen da suka san gaskiya, ba za a goge su ba.”

A nasa É“angaren, Lauyan Buba, Rabi’u Sidi, ya zargi kotun da jingine Lauyoyin mai Æ™ara. Domin su ma kawai sun ji labarin yanke hukuncin ne, ba su ma san an yi.

Ya ce, “Ba a sanar da mu zaman kotun ba. Babu wanda ya ce mana za a yi zama, kawai mun ji labarin hukuncin ne a cikin labarai.”

Lauyan ya ƙara da cewa tawagar Lauyoyin za ta yi taro domin sanin matakin da za su ɗauka na gaba.

Bayan da wancan labarin ya fita, Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya dakatar da Kwamishinan daga kan muƙaminsa, to amma bayan yanke wannan hukunci, gwamnan ya mayar da Sankara kan kujerarsa.

 

No comments