Daga Ibrahim Muhammad, Kano An yaba wa Asibitin ALBARKA a ƙarƙashin kagorancin Dakta Muhammad N.Salihu bisa ƙoƙarin da suke yi na taimakon a...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An yaba wa Asibitin ALBARKA a ƙarƙashin kagorancin Dakta Muhammad N.Salihu bisa ƙoƙarin da suke yi na taimakon al’umma marasa ƙarfi ta ɗaukar nauyin kula da lafiya a tsakanin al'umma kyauta a ɓangarorin lafiya daban-daban.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Dala, Alhaji Surajo Ibrahim Imam ne ya yi yabon a lokacin da tawagar jami’an asibitin suka kai masa ziyarar ban-girma a ofishinsa.
A nasa jawabin, Alhaji Surajo ya bayyana shugaban Asibitin, Dakta Muhammad Nuhu Salihu da cewa tun yana matsayin Daraktan kula da lafiya a asibitin ƙashi na Dala yake tallafa wa al’ummar yankin.
Ya kuma ba shi tabbacin yin haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin Ƙaramar Hukumar Dala da Asibitin ALBARKA wajen inganta harkokin kiwon lafiya ga mazauna Dala.
A nasa jawabin, Dakta Muhammad N. Salihu , shugaban Asibitin na ALBARKA ya bayyana cewa ziyarar da suka kai Ƙaramar Hukumar ta Dala, ziya ce ta taya Alhaji Surajo Imam murnar zaɓen da aka yi masa da rantsar da shi a matsayin shugaban Ƙaramar Hukuma.
Ya kuma tabbatar wa shugaban na Dala cewa Asibitin ALBARKA zai himmatu wajen tallafa wa gwamnatin sa domin bada gudunmuwa wajen inganta lafiya.
A nan ne ya sanar da wani shiri da asibitin nasa zai gudanar na aikin tsaftace haƙora da dasa haƙora kyauta ga mazauna Ƙaramar Hukumar mutum 300.
Dakta Muhammad N. Salihu ya ce duba lafiyar haƙoran zai shafi masu ƙaramin ƙarfi ne, an kuma tsara shirin, wanda za a yi nan da ƙarshen wannan shekara, ko kuma a farkon watannin sabuwar shekara mai zuwa.
Da yake bayani kan haƙora, masanin ilimin haƙora Malam Kabiru Ɗalha ya bayyana rashin wayar da kan al’umma kan tsaftar haƙori na daga cikin abin da ya sa mutane ke sakaci, wanda hakan kan iya yin illa ga lafiyarsu.

No comments