Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana Manjo Hamza Almustapha da cewa mutum ne da yake da inganci da son ci gaban ƙasa da zai iya samar da k...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana Manjo Hamza Almustapha da cewa mutum ne da yake da inganci da son ci gaban ƙasa da zai iya samar da kyakkyawan jagoranci da fitar da al'ummar ƙasar nan daga yanayi na ƙuncin rayuwa.
Shugaban 'Network for better' da ke fafutukar ganin Manjo Hamza Almustapha ya zama shugaban ƙasar Nijeriya, reshen jihar Kano Mustapha Ɗahiru ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Ya ce, su suna da yaƙinin cewa Almustapha zai iya kawo sauyi a halin da ake ciki a ƙasar nan, domin waɗanda suke da tunani a da na ganin ba zai iya ba, yanzu sun yarda sun tabbatar zai iya cikin ikon Allah.
Ya ce, da ma Hausawa na cewa Juma'ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake ganeta. To tuni sun gane hakan akan Almustapha, suna yi masa kyakkyawan fata, ko ta ina masoya sai ƙaruwa suke.
Alhaji Mustapha Ɗahiru ya ce tun da suka soma wannan fafutuka akan Hamza Almustapha sai akhairi suke gani ta ko'ina, ciki da wajen ƙasar nan mutane na ta addu'a akan nasarar tafiyar.

No comments